34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Zaɓen 2023: Ku taimaka ku ba yankin mu kujerar shugaban ƙasa, wata ƙungiyar Inyamurai

LabaraiZaɓen 2023: Ku taimaka ku ba yankin mu kujerar shugaban ƙasa, wata ƙungiyar Inyamurai

Wasu masu ruwa da tsaki daga yankin kudu masu gabas na Najeriya, a ranar Juma’a sun roƙi ‘yan Najeriya, jam’iyyun siyasa da sauran yankunan ƙasar nan da su tabbatar cewan yankin kudu maso gabas ya samu kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 mai zuwa, domin samar da daidaito da kuma adalci. Jaridar Daily Trust ta rahoto

Ƙungiyar za ta gana da manyan ‘yan siyasa akan ƙudirin ta

Masu ruwa da tsakin a ƙarƙashin Greater Nigeria Conference (GNC), a wata sanarwa da darektan watsa labaran su, Collins Steve Ugwu, ya fitar, sun bayyana cewa za su tattaro manyan ‘yan siyasa maza da mata daga sauran yankunan ƙasar nan domin tattaunawa akan lamarin a ranar 25 ga watan Afrilu.

Waɗanda za a gayyato, a cewar Ugwu, sun haɗa da masu neman takarar shugaban ƙasa daga yankin kudu maso gabas, gwamnonin yankin, wakilai daga kungiyar Ohanaze Ndigbo, ƙungiyar Yarbawa, ƙungiyar dattawan Arewa da sauran su.

Babban maƙasudin wannan taron shine domin ƙasar mu Najeriya, wajen ganin an samar da shugabanci mai kyau da adalci a tsakanin mu ta hanyar damawa da kowa a siyasar ƙasa.

Muna maraba da shahararrun baƙin mu a wajen wannan taro waɗanda su ka haɗa da tsohon gwamnan jihar Enugu, Dr Okwesilieze Nwodo da sanata Victor Umeh, dukkanin su tsofaffin shugabannin wasu manyan jam’iyyu a Najeriya, a matsayin shugabannin shirya wannan taron na GNC, domin roƙon ‘yan Najeriya da su ba yankin kudu maso gabas damar kafa tarihi a Najeriya. A cewar wani ɓangare na sanarwar.

Zaɓen 2023: Dole ne shugaban ƙasa ya fito daga kudancin Najeriya -wata ƙungiya ta magantu

Wata ƙungiya mai suna Defense for Yoruba People’s Rights, tayi kira da jam’iyyun Peoples Democratic Party (PDP) All Progressives Congress (APC) da sauran jam’iyyu kan cewa su zaɓo ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023 daga yankin kudancin Najeriya.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Otunba Muyideen Olamoyegun, ya fitar a birnin Akure, na jihar Ondo ranar Talata. Jaridar Punch ta rahoto.

Ƙungiyar ta bayyana cewa yin adalci ne kai kujerar shugaban ƙasa yankin kudu, inda ta jajirce cewa lallai dole ne jam’iyyun APC, PDP da sauran jam’iyyu su zaɓo yan takarar su daga yankin kudu domin tabbatar da daidaito.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe