34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Shekaruna 2 ina kokarin shawo kanta har ta amince ta aureni, Mijin Bilkisu, Amaryar shekarun baya mai lalurar kafa

LabaraiShekaruna 2 ina kokarin shawo kanta har ta amince ta aureni, Mijin Bilkisu, Amaryar shekarun baya mai lalurar kafa

Shirin BBC Hausa na Mahangar Zamani ya samu damar tattaunawa da Bilkisu da mijinta Suleiman, inda suka bayyana kalubalen da suka fuskanta kafin aurensu ya tabbata.

Ta fara da bayyana cewa bata yi tunanin da gaske yake ba saboda akwai wadanda sukan je wurinta kamar da gaske daga baya kuma su shiririce.

cute couple
Shekaruna 2 ina kokarin shawo kanta har ta amince ta aureni, Mijin Bilkisu, Amaryar shekarun baya mai lalurar kafa

A cewarta, a baya ta cire rai daga yin aure saboda lalurarta, amma sai ga shi Ubangiji ya azurtata da wanda ya ke son aurenta da gaske.

A bangarensa, kamar yadda ya shaida wa BBC Hausa, ya ce ya fara sonta ne bayan ta yi tsokaci a wani hotonsa, sai ya duba wasu wallafe-wallafenta a shafinta na kafar sada zumuntar zamani wanda take ba masu irin lalurarta kwarin guiwa.

A cewar mijin:

“Wallahi da na ga comment dinta a karkashin hoton da ni da mufti nayi, sai na bi fejinta sai na ganta. Daga nan dai kawai sai ta burge ni kai tsaye.

“Daya daga cikin dalilan shi ne, ba kasafai zaka ga mutum mai lalura ta musamman ba wanda zai tsaya wa kansa ba, har ma ya tsaya wa masu lalura irin tashi ba.

“Anan na ganta sai nace a’a gaskiya daga yau dai na zama masoyin abubuwa da kike yi da rubuce-rubuce da kike yi na kara wa mutane kwarin guiwa da kike yi. Kina burge ni, Allah ya taimaka.”

Ta fara da shaida yadda ta fara soyayya da wani likitanta wanda a lokacin da ta daina zuwa asibiti yake zuwa gida yana duba ta.

Kamar yadda ta ce:

“Shi likitana ne. A lokacin na daina zuwa asibiti, yana zuwa gida yana yi min. Sai a hankali ya fara nuna yana sona, don a lokacin aure ya fita a raina saboda gani nake yi ba zan taba aure ba.

“Kuma gani nake yi kamar wasa yake yi min saboda akwai wadanda zasu zo suce suna sonka, azo a dinga maka wasa da hankali daga baya su rabu da kai.

“To shi da ya nuna yana so sosai, sai nace to shikenan, ya gabatar da kan shi shima ya ce zai je gida ya yi musu magana.

“Da ya je gida ya yi magana, maman shi ta ce bata yarda ba. Ni kuma nace wallahi na hakura. Ya yi ya yi, nace a’a na hakura saboda ba zan iya aurenshi iyayenshi ba sa so ba.”

A lokacin da take soyayya da likitan, suna tare da Suleiman, mijinta na yanzu.

Kamar yadda mijin ya bayyana, sai da ya kwashe shekaru 2 yana kokarin shawo kanta, dakyar ta amince don da farko ta ce ta hakura da soyayya

Ya ce so da kauna ne suka sa ya jure ya kuma jajirce duk da wahalar da ya sha kafin ya samu ta amince ta aure shi.

Uwargida ta hau kujerar naki ta ki amincewa da mijinta har sai an yiwa amarya gwajin cuta mai karya garkuwan jiki

Uwargida ta ce sam bata aminta da amaryar mijin ta ba har sai anyi gwaji

Wata uwar gida a garin Kano, ta ki amincewa da mijinta saboda ta na zargin ya auro amarya ba tare da an yi gwajin cuta mai karya garkuwan jiki ba.

Tuni Uwar gidan ta garzaya wurin hukumar Hisba da ke jihar Kano inda ta kai kukanta, ita kuma hukumar Hisab batayi kasa a gwiwa ba ta gayyato ma’auratan,inda aka yi musu gwaji, sai dai har yanzu hukumar ta Hisba ba ta bayyana sakamakon gwajin ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe