28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Hotunan rusheshiyar diyar Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, da angonta sun bada kala

LabaraiHotunan rusheshiyar diyar Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, da angonta sun bada kala

Diyar Gwamna Hopr Uzodinma na Jihar Imo, Oprah Chioma Uzodinma ta auri masoyinta, Henry Ihaeri.

An daura auren nasu ne a kotun aure ta tarayya dake Abuja, LIB ta ruwaito..

amarya rusheshiya
Hotunan rusheshiyar diyar Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, da angonta sun bada kala

Daga Gwamna Uzodimma har matarsa, Chioma sun halarci taron.

Mahaifiyarta ta wallafa hotunan auren tare da yin tsokaci karkashin wallafar, kamar yadda Chioma Uzodimma ta wallafa:

“Tsawon shekaru, muna ganin yadda kyakkyawar diyarmu, Oprah Chioma Uzodimma da masoyinta, Henry Ohaeri suka dade suna son junayensu. Ganin su suna furta alkawuran aure a tare jiya a Kotun aure ta tarayya da ke Abuja ya yi matukar faranta min rai.”

Ta ci gaba da bayyana farin cikinta tare da yi musu fatan alkhairi inda ta bayar da tabbaci akan cewa ta san zasu hada kansu su zauna lafiya cikin kwanciyar hankali.

Kano: Anyi ram da babban abokin ango bayan ya sunkuce akwatinan amarya masu ƙimar N500,000

Lamarin ya auku ne a yankin Gaida da ke ƙaramar hukumar Kumbotso ta Jihar Kano, bayan mako ɗaya da bikin, LIB ta ruwaito.

Shugaban ƴan sakan Gaida, Shekarau Ali ya ce, an kama aminin angon da mukullen gidan ma’auratan bayan angon ya kai ƙorafi.

Yayin da aka kamashi, wanda ake zargin ya bayyana yadda ya samu mukullan daga hannun ƴan uwan amaryar bayan ya musu ƙaryar zai kai wa angon.

Ali ya ƙara da cewa:

“Angon ya buƙaci da ya maido da makullen, amma ya yi burus dashi. Bayan tabbatar fitarsu daga gidan, ya buɗe gidan ya kwashe akwatinan auren da kayan abinci.”

Za a mika shi hannun ‘yan sanda da zarar an kammala bincike

Shugaban ƴan sakan ya cigaba da bayyana yadda suke bincikarsa, daga bisani zasu miƙasa ga ƴan sanda.

Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya ce sheɗan ne ya zugashi ya ci amanar abokinsa. Sannan ya nemi gafara.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe