27.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Jarumin fim mai shekaru 81, Al-Pacino, ya na zuba soyayya da budurwa mai shekaru 28

LabaraiJarumin fim mai shekaru 81, Al-Pacino, ya na zuba soyayya da budurwa mai shekaru 28
6257bb62ade762
Jarumin fim mai shekaru 81, Al-Pacino, ya na zuba soyayya da budurwa mai shekaru 28

Jim kadan bayan an hangi jarumi Al Pacino, dan kimanin shekaru 81, a wata liyafar cin abinci tare da wata matashiya mai suna Noor Alfallah, mai shekara 28, an gano cewa sun ashe sun dade suna zuba soyayya.

Tace duk da bambancin shekaru da ke tsakanin su suna matukar kaunar junan su

6257bb7e1fcfe3
Al-picano tare da masoyiyar sa

Masoyan biyu da suka kasance ruwa biyu rabi Amurkawa rabi kuma ‘yan kasar Kuwait wanda suka kasance sun fito daga manyan gidaje masu yalwatuwar arziƙi, an hangi masoyan ne tare a wata liyafar cin abinci da aka gudanar don nune-nunen zanen Julian Schnabel.
Da take magana da kafar Hello jim kadan bayan ta bayyana soyayyarta da Al-Picano, inda ta ce ‘ko kadan ba ta nadamar’ soyayyar su duk da banbancin shekaru dake tsakanin su.
Noor ta kara dacewa ”Shekarunmu ba abin damuwa bane. Munbi zabin zukatan mu ne ita kuma zuciya ba ta san abin da take gani ba, kawai abinda take ji ta sani wannan ce soyayya ta ta farko, hakan na kayar dani.’
Ta kara da cewa: Duk da shekarun sa ya fi ni lafiya sosai. Ina girmama shi sosai.’
Ta kara da cewa soyayyar su ta samo asaline tun lokacin da aka kakaba dokar kulleb annobar Corona.

So makaho ne: Matashi mai shekaru 25 ya daura dammarar yin wuff da tsohuwa

Ba tare da dubi da tazarar shekaru 60 din da ke tsakaninsu ba, wani matashi ɗan shekara 25 ya faɗa kogin son wata tsohuwa mai shekaru 85 mai suna Thereza.

Masoyan biyu, Thereza da Muyiwa sun shirya rayuwar aure duk da ƴaƴan masoyiyarsa da abokansa sun nuna rashin amincewarsu.
Muyiwa ya bayyana wa Afrimax a wata tattaunawar da suka yi yadda ya bar ƙasarsa ta Congo don karatu a jami’a inda ya kama gidan hayan Thereza tare da abokinsa.

Saurayin ya ce, a baya ya yi soyayya da ƴan mata bai jidaɗi ba, amma Thereza ta bambanta da sauran mata, sannan yana tsoron kada ta mutu da wuri.
Ya ce tana kyautata masa

Kamar yadda ya shaida:

“Ina tuna ranar wata Juma’a sanda abokin zama na yayi nisan kiwo, yunwa ta kama ni, gashi bamu da abinci.

“Na galabaita kwarai. Kawai sai tsohuwar ta kawo min abinci. Yadda ta tarairaye ni ne yasa na tsunduma a kogin soyayyarta.”

“Duk da tsohuwa ce wacce tayi jika dani, amma ina matukar kaunarta.”

Yayi kira ga masu sukarsa da su sakar masa mara ya yi fitsari, saboda wacce yake ƙauna, inda yace:
Wannan ra’ayina ne, kuma shine muradi na.”

Sun kusa shigewa daga ciki

Thereza ta bayyana tsananin ƙaunar da take wa Muyiwa kamar yadda shima yake sonta. Ta ce a shirye take da tayi wuff dashi.

A cewarta:

“Shekaru na 85. Ina da ƴaƴa 8 da jikoki 20. Idan za’ayi dubi da shekarun saurayi na, kusan sa’an jikana na biyar ne. Amma muna ƙaunar juna. A shirye nake da in zama matarsa.”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe