27.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Matashi ya kashe babban abokinsa, ya tsere da motarsa da makuden kudaden sa a jihar Neja

LabaraiMatashi ya kashe babban abokinsa, ya tsere da motarsa da makuden kudaden sa a jihar Neja
62581470b11ab
Hassan Shehu matashin da abokin sa ya kashe

Wani dan kasuwa mai suna Hassan Shehu, mai Kimanin shekaru 25, ya rasa ransa ta sanadiyyar abokinsa a unguwar Tudun-Fulani da ke karamar hukumar Bosso dake jihar Neja.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Wasiu Abiodun, shine ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis 14 ga watan Afrilu 2022.

Ya kirashi akan yazo zasu kulla ciniki

A ranar 12/04/2022 da misalin karfe Biyar ne muka samu kiran gaggawa cewar an tsinci gawar wani saurayi a wani gida da ke unguwar Tudun-Fulani a karamar hukumar Bosso,” inji shi kakakin rundunar ‘yan sandan.
Jami’an ’yan sanda da ke aiki da sashen Bosso ba su bata lokaci ba inda suka dira a wurin da lamarin ya faru, na take aka gano gawar, inda daga bisani aka bayyana sunan mamacin da Hassan Shehu,wanda ya kasance dan kasuwa ne a kasuwar Kure,da ke garin Minna.
Binciken farko ya bayyana cewa wani abokinsa mai suna Bashir ne ya caka masa wuka a wuya.

Wanda ya aikata laifin ya tsere

Hukumar ta PPRO ta ci gaba da cewa, ana nan ana gudanar da bincike a kan lamarin, yayin da ake kokarin ganin an cafke wanda ake zargi.
A yanzu haka ‘yan uwa da abokai sun bazama shafin sada zumunta na Facebook don yada hotunan wanda ake zargi da aikata kisa.
A cewar wani mai suna Kira Miraj King, wanda ake zargin ya yaudari marigayin akan yazo gidan sa da ke Tudun Fulani da sunan yanada zinare na sayarwa.
Kanin marigayin ya bayyana cewa wanda ake zargin ya umurci marigayin da ya zo da kudi kimanin Naira Miliyan 5 amma sai marigayin yace shi Naira Miliyan 3.5 kawai ya ke da shi.
Da isarsa gidan, Bashir bai tsaya wata-wata ba kawai ya daba wa Hassan wuka wanda hakan yayi ajalin sa har lahira sannan ya gudu da motarsa, wayoyi biyu da kuma kudi Naira Miliyan uku da rabi.
Ga sakon da ‘yan uwa da abokan arziki suka wallafa a shafin facebook:

625816a34a8c93
Wanda ake zargi da aikata laifin kisar


Wannan shi ne Bashir don Allah idan ka gan shi a ko’ina a jihar Neja ko kuma a fadin Najeriya a kamashi mai laifi ne kuma mai kisan kai ne ya kashe babban abokinsa a ranar Talata 12/4/2022. Ya kira babban abokinsa a waya Ya yi masa karya cewa yana da zinare da zai sayar sai abokin nasa ya zo unguwar dake tudun fulani gabas, Boso, Minna, Niger jihar Nija,inda Bashir da wasu abokansa biyu suka shirya suka kashe babban abokinsa inda suka daba masa wuka, sannan ya kwashe kudin da ke tare da shi ya gudu da motarsa, wayoyi guda biyu da zinare, Ya Allah ya Gafarta Maka Hassan.

Matar aure ta sa ‘yan daba sun sace ‘yar Adama ta Dadin Kowa, sun yayyanketa saboda tana soyayya da mijinta

Zahra’u Sale, wacce aka fi sani da Adama ta Dadin Kowa ta bayar da labari mai ban tausayi a shafinta na TikTok kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Gidan rediyon Premier da ke Kano ma sun kawo rahoton inda suka ce wata matar aure da kawarta sun dauko hayar ‘yan daba sun je sun dauke Fa’iza Ja’afar wacce ‘ya ce ga Adama suka tafi da ita wani kango suka yayyanke ta sannan suka ja mata kunne akan ta rabu da mijin matar.
An samu nasarar damke matar auren da kawarta yayin da ita kuma Fa’iza ta ke kwance a gadon asibiti tana samun kulawa daga raunukan da suka ji mata.

Adama ta wallafa bidiyon wannan rahoton a shafinta na TikTok kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta nuna sannan ta rubuta “Ku taya ni jaje”, inda cikin rahoton wakilin gidan rediyon ya ce sun samu zantawa da Fa’iza, mijin matar da kuma ita Adaman, ga cikakken rahoton.
Cikakken rahoto

Kamar yadda wakilin ya ruwaito, an gurfanar da mutane 4 a gaban kotun majistare da ke Dawakin Tofa bisa zarginsu da cin zarafin wata Fa’iza Ja’afar.

Wakilin gidan rediyon Premier ya fara da cewa:

“Da fari dai an zargi Sumayya Idris da hada kai da kawarta, Aisha Yunus wadanda suka yi hayar ‘yan daba suka kama Fa’iza suka kai ta wani wuri, suka yi mata duka tare da yankarta a wuri daban-daban a jikinta.

“An samu bayanai akan yadda Sumayya Idris ta zargi Fa’iza Ja’afar da yin soyayya da mijinta. Hakan yasa suka hada kai da kawarta Aisha Yunusa wadanda suka dauki hayar ‘yan daba don su koya mata hankali.
Sai dai bayan da abin ya faru ne ‘yan uwan Fa’iza sun kai kara ofishin ‘yan sanda da ke Unguwa Uku, inda aka kama wadanda suka yi aika-aikar ciki har da wadanda suka aikata mummunan aikin har da wani Umar da Hussain.”

Kamar yadda wakilin gidan rediyon Premier ya shaida, duk wadanda ake zargin sun amsa laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa.

Alkalin kotun, Al-Qasim Danfillo ya yanke wa wadanda ake zargin biyan tarar dubu goma-goma a ko wanne laifi da suka aikata ko kuma daurin watanni uku uku, kenan idan an hada wata tara.
Alkalin kotun, Al-Qasim Danfillo ya yanke wa wadanda ake zargin biyan tarar dubu goma-goma a ko wanne laifi da suka aikata ko kuma daurin watanni uku uku, kenan idan an hada wata tara.

A laifi na hudu kuwa alkalin ya yanke musu shekara daya a gidan yari ko kuma biyan tarar N20,000 ko wannensu.

Har ila yau, alkalin ya umarci su biya Fa’iza kudin magani, N50,000 ko zaman gidan yari na watanni 6 sannan su ci gaba da daukar nauyin kudin maganinta har ta samu lafiya.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe