34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Saura ƙiris mu magance matsalar tsaro a Najeriya, Shugaba Buhari

LabaraiSaura ƙiris mu magance matsalar tsaro a Najeriya, Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa lokacin bukukuwan Easter na bana ya sanya ‘yan Najeriya sun yarda da cewa matsalar tsaro da halin ɗar-ɗar da ake fama da shi a ƙasar nan ya kusa zama tarihi. Jaridar Daily Trust ta rahoto

Shugaba Buhari ya aike da saƙon Easter

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a saƙon Easter na shekarar 2022 da ya aikewa ‘yan Najeriya.

Ya bayyana cewa yakamata ‘yan Najeriya su yi la’akari da tsaro da haɗin kan ƙasa wajen furta kalaman su yayin da ƙasar ta ke tunkarar lokutan zaɓuɓɓuka.

Ya bayyana cewa wannan lokacin ya sanya wa ‘yan Najeriya jajircewa wajen ganin guiwoyin su ba su sare ba duk kuwa da ƙalubalen da su ke fuskanta a rayuwa.

Ya buƙaci ‘yan Najeriya su so junan su

Shugaba Buhari ya roƙi ‘yan Najeriya da su cigaba da ƙaunar junan su maimakon nuna ƙiyayya ga juna, da kuma cigaba da nuna kishin ƙasa, inda ya ke cewa “wannan ce ƙasar da kawai mu ke da ita”

Bikin wannan shekarar yana da muhimmanci ga manyan addinai biyu da mu ke da su a Najeriya. Ya haɗa kwanaki 40 ga kiristoci, inda ake buƙatar mutum yayi azumi, ibada, taimakon talakawa, ƙyamatar rashin adalci da husuma da kuma tuba kan zunubai.

Waɗannan ɗabi’un haka ake son su a wurin musulmai, waɗanda su ke tsaka da gudanar da azumin watan Ramadan.

A matsayin mu na ƙasa daya, saƙon Easter wanda ya ambaci tashin Yesu bayan giciyewa da binne shi, yana tuna mana da ƙarfin ƙaunar ubangiji, imani da kuma fansa.

Tun kafuwar Najeriya ba a taɓa samun ingantaccen shugaba irin shugaba Buhari ba -Gwamna Masari

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa tun lokacin da aka haɗe Najeriya a 1914, ƙasar bata taɓa samun ingantacciyar gwamnati da shugaban ƙasa irin shugaba Buhari ba. Jaridar The Guardian ta rahoto

Gwamnan ya faɗi haka ne ranar Asabar a Katsina yayin wani gangami wanda masu amfana da shirin gwamnatin tarayya na ‘Social Investment Programme’ (NSIP), na jihar su ka shirya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rahoto cewa, an shirya gangamin ne a ƙarƙashin jagorancin shugabannin ‘Social Protection and Good Family Value Initiative’ (SPGFVI).

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe