Zahra’u Sale, wacce aka fi sani da Adama ta Dadin Kowa ta bayar da labari mai ban tausayi a shafinta na TikTok kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.
Gidan rediyon Premier da ke Kano ma sun kawo rahoton inda suka ce wata matar aure da kawarta sun dauko hayar ‘yan daba sun je sun dauke Fa’iza Ja’afar wacce ‘ya ce ga Adama suka tafi da ita wani kango suka yayyanke ta sannan suka ja mata kunne akan ta rabu da mijin matar.

An samu nasarar damke matar auren da kawarta yayin da ita kuma Fa’iza ta ke kwance a gadon asibiti tana samun kulawa daga raunukan da suka ji mata.
Adama ta wallafa bidiyon wannan rahoton a shafinta na TikTok kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta nuna sannan ta rubuta “Ku taya ni jaje”, inda cikin rahoton wakilin gidan rediyon ya ce sun samu zantawa da Fa’iza, mijin matar da kuma ita Adaman, ga cikakken rahoton.
Cikakken rahoto
Kamar yadda wakilin ya ruwaito, an gurfanar da mutane 4 a gaban kotun majistare da ke Dawakin Tofa bisa zarginsu da cin zarafin wata Fa’iza Ja’afar.
Wakilin gidan rediyon Premier ya fara da cewa:
“Da fari dai an zargi Sumayya Idris da hada kai da kawarta, Aisha Yunus wadanda suka yi hayar ‘yan daba suka kama Fa’iza suka kai ta wani wuri, suka yi mata duka tare da yankarta a wuri daban-daban a jikinta.
“An samu bayanai akan yadda Sumayya Idris ta zargi Fa’iza Ja’afar da yin soyayya da mijinta. Hakan yasa suka hada kai da kawarta Aisha Yunusa wadanda suka dauki hayar ‘yan daba don su koya mata hankali.
“Sai dai bayan da abin ya faru ne ‘yan uwan Fa’iza sun kai kara ofishin ‘yan sanda da ke Unguwa Uku, inda aka kama wadanda suka yi aika-aikar ciki har da wadanda suka aikata mummunan aikin har da wani Umar da Hussain.”
Kamar yadda wakilin gidan rediyon Premier ya shaida, duk wadanda ake zargin sun amsa laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa.
Alkalin kotun, Al-Qasim Danfillo ya yanke wa wadanda ake zargin biyan tarar dubu goma-goma a ko wanne laifi da suka aikata ko kuma daurin watanni uku uku, kenan idan an hada wata tara.
A laifi na hudu kuwa alkalin ya yanke musu shekara daya a gidan yari ko kuma biyan tarar N20,000 ko wannensu.
Har ila yau, alkalin ya umarci su biya Fa’iza kudin magani, N50,000 ko zaman gidan yari na watanni 6 sannan su ci gaba da daukar nauyin kudin maganinta har ta samu lafiya.
Sheikh Pantami Baba na ne, Jaruma Adaman Kamaye ta Dadin Kowa
Jaruma Zahra’u Saleh Pantami wacce aka fi sani da Adaman Kamaye a shiri mai dogon zango na Dadin Kowa wanda ake haskawa a tashar arewa 24 ta bayyana alakar da ke tsakaninta da ministan sadarwa, Sheikh Ali Isa Pantami a wata tattaunawa da jaridar Aminiya ta yi da ita.
Kamar yadda ta bayyana, ita ‘yar asalin jihar Gombe ce kuma ta yi karatun firamare da sakandare a Gombe.
Ta bayyana cewa duk wanda aka ji sunansa akwai Pantami dan gidansu ne kuma Sheikh Isa Ali Pantami kanin mahaifinta ne.
A cewarta ta shiga harkar fin ne ta uwar dakinta, Hajiya Zulai Bebeji saboda sun zauna tare a Saudiyya don haka bayan sun dawo ta bayyana mata burinta na shiga fim.
Ta bayyana yadda ta hada ta da Musa Mai Sana’a wanda ya sa ta a fim dinsa mai suna Hisabi daga nan ta shiga shirin fim din sosai bayan marigayi Sani SK da Alasan Kwalle sun zama mata tsayayyu biyu a industiri.
Ta bayyana yadda ta je tantancewar shiga shirin fim din Dadin Kowa na tashar Arewa 24 wanda tace sun fi mutane 70 amma ta ci nasarar zama zakakurar da aka zaba.
Ta bayyana alakar da ke tsakaninta da Kamaye inda tace mutunci ne kawai kuma yana mata gyara idan ya ga ta yi kuskure amma babu wata alakar soyayya a tsakaninsu.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com