24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Kaduna: Matashi da yayi ba-haya a Masallaci kan N20k ya gurfana a kotu

LabaraiKaduna: Matashi da yayi ba-haya a Masallaci kan N20k ya gurfana a kotu

Wata kotun Shari’ar musulunci a Magajin Gari, cikin jihar Kaduna, a ranar Alhamis ta bayar da umurnin a sakaya wasu mutum biyu, Nura Usman da Adamu Dauda a gidan gyaran hali bisa zargin yin bahaya a masallaci.

Jaridar Punch ta rahoto daga The News Agency Of Nigeria (NAN) cewa ‘yan sanda sun tuhumi Nura Usman da Adamu Dauda da laifin cutar da al’umma da kuma tada zaune tsaye.

An ɗaga sauraron ƙarar

Alkalin kotun, mai Shari’a Malam Rilwanu Kyaudai, ya ɗaga sauraron Shari’ar har zuwa 28 ga watan Afrilu domin bai wa ‘yan sanda damar kawo shaidun su.

Mutanen unguwa sun miƙa su hannun hukuma

Tun da farko, mai shigar da ƙara, sifeto Ibrahim Shuaibu, ya bayyana cewa mutanen unguwar ne su ka miƙa Usman da Dauda a hannun ‘yan sanda a ofishin su na Tudun Wada a ranar 11 ga watan Afrilu.

Ya bayyana cewa an cafke Usman yana bahaya a masallaci a Alkalawa Road, Tudun Wada, Kaduna da misalin ƙarfe 2 na rana.

Ya bayyana cewa wanda ake ƙara na biyun, Dauda, yayi alƙawarin ba Usman N20,000 domin yayi bahaya a masallacin.

An amince da yin buda baki a masallacin Harami da na Annabi(SAW) bayan shekaru 2 da dakatarwa

A yayin shirye-shiryen maraba da watan Ramadan, shugaban hukumar kula da masallatan harami guda biyu ya sanar da cewa an bayar da izinin gudanar da liyafar buɗa baki a masallacin Harami bayan dakatarwar da aka yi na tsawon shekaru biyu sakamakon annobar COVID-19, theislamicinformation.com ta ruwaito.

An kuma sabunta izini ga masu samar da abinci mai saurin gaske a wuri mai tsarkin

Fadar shugaban ƙasar ta kuma sanar da cewa an bayar da izinin dawo da buɗa baki a masallacin Annabi da ke Madina.

Ana sa ran masallatan Harami guda biyu za su tarbi ɗimbin masu ibada a lokacin Umrah a Masallacin Harami da ziyartar masallacin Annabi a cikin watan Ramadan, wanda za a fara a farkon watan gobe.

Hukumomin Saudiyya sun sassauta dokokin gudanar da aikin Umrah a baya-bayan nan bayan wani mataki da masarautar ta dauka, wanda kuma ya sassauta takunkumin hana yaɗuwar cutar COVID-19.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe