36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

An bude karin manyan zaurukan sallah 80 na Masallacin Harami a watan Ramadanan bana

LabaraiAn bude karin manyan zaurukan sallah 80 na Masallacin Harami a watan Ramadanan bana

Shugabannin koli na masallatan Makka da Madina ya sanar, a ranar 5 ga watan Afirilu cewa, masallacin haramin Makka ya bude karin zaurukan sallah kimanin 80 a karon farko, a watan Ramadan na wannan shekara.

Wannan bude karin zaurukan sallah a masallacin, na daga cikin wani rukuni na sake fadada masallacin haramin na Makka.

Masjid Al Haram
An bude karin manyan zaurukan sallah 80 na Masallacin Harami a watan Ramadanan bana

A fadar daraktan mulki mai kula da sha’anin fadada masallacin, Walid Al-Masoudi, yace sababbin zaurukan an yi su ne a bangaren karkashin kasa na masallacin, hawa na farko, da kuma kananan dandamalai na tsakanin manyan gine-ginen masallacin, wadanda za’a iya samun su a ko wacce kusurwa ta ko wacce mashiga ta masallacin.

Kamar yadda jaridar Arab News ta bayyana, karin zaurukan sallar, ya samar da kaso 95 na gabaki daya abin da masallacin zai iya dauka na yawan masu ibada, inda zai iya daukar kimanin masu ibada mutum 300,000. Idan kuma aka kammala aikin zaurukan cikin masallacin, za’a mayadda masu ibada bangaren farfajiyar Arewa, wanda shi kuma zai iya daukar kimanin masu ibada 280,000 ; bayan haka, akwai ma wasu zaurukan a farfajiyar yamma da masallacin.

Haka kuma, Al Masoudi din, ya bayyana cewa adadin masallata yana kara nunkuwa ne daga lokaci zuwa lokaci a watan Ramadan. Saboda haka an sanya ma’aikata na musamman su tabbatar da samarwa jama’a sararin walwala da kai kawo, tare da samar da guraben sallah, ta yadda masu ibada zasu iya shiga ko ina su fita lami-lafiya .

Ya jaddada cewa ana gudanar da aikin ne karkashin mataimakin babban sakataren ayyukan filaye da kare muhalli, Mohammed Al Jabri, na hukumar koli ta sha’anin masallatan Harami wanda
Sheikh Abdulrahman Al-Sudais yake jagoranta.

Babban hadafin, Masarautar shine ta samar da ingantacciyar hidima ga baki masu zuwa ibada.

Za’a iya samun sababbin zaurukan a babbar mashigar masallacin, wato King Abdullah mashiga mai lamba ta 100, da lamba ta 104, 106, 112, 173, 175, da kuma lamba ta176. A bangaren Arewa da kuma mashiga ta 114, 116, 119, 121 da kuma ta 123, wadanda suke a bangaren yamma da kuma mashiga ta 162, 165, da ta 169 A bangaren gabas.

Allahu Akbar: Bayan shekaru 88, za a yi sallar Taraweehi a masallacin Hagia Sophia

Labari mai dadi na isowa daga babban masallacin Hagia Sophia da ke kasarTurkiyya a birnin Istanbul, wanda ya dawo da matsayinsa na masallaci shekaru biyu kacal da suka wuce.

Kamfanin dillancin labaran Anadolu ya labarta cewa, babban masallacin Hagia Sophia na shirin gudanar da sallar tarawihi na farko a cikin watan azumin Ramadan na bana, bayan shafe shekaru 88 ana amfani da shi a matsayin gidan tarihi.

Bayan shafe shekaru mai tsayi masallacin zai dawo da ayyukan ibada a watan Ramadan Bana

Ba wai sallar tarawihi kadai ba, an ruwaito cewa, masallacin Hagia Sophia ya kuma shirya gudanar da taruka da dama na watan Ramadan kuma ana sa ran masu ibada da yawa za su ziyarci wurin a cikin wannan wata mai alfarma.

Masallacin a baya ya kasance gidan adana kayan tarihi

Masallacin Hagia Sophia a baya ya kasance a matsayin gidan tarihi ne tun shekarar 1934. Amma, a shekarar 2020 ya dawo da babbar martaba a matsayin masallaci kuma an bude shine domin musulmi su gudanar da ibada a shekarar 2020.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe