34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Gurneti ya tashi a masallacin da ya fi kowanne girma a Kabul, ya jigata mutum 6

LabaraiGurneti ya tashi a masallacin da ya fi kowanne girma a Kabul, ya jigata mutum 6

Wani bam ya tarwatse a yayin da masallata ke tsaka da sallar azahar , a babban masallacin Kabul, a ranar Laraba.

Kafofi da yawa sun ruwaito cewa mutane 6 sun yi mummunan rauni, a wannan hari na rashin mutuncin.

Mai magana da yawun hukumar yan sanda na Kabul Khalid Zadran, yace, an kama wani mutum daya da ake zargin yana da hannu a harin masallacin na Pul-e-Khisti.

Kabul Mosque
Gurneti ya tashi a masallacin da ya fi kowanne girma a Kabul, ya jigata mutum 6

Babu wanda ya dauki nauyin harin kawo yanzu, amma wannan shine harin gurneti na biyu a cikin kasa da sati daya.

A wani hari da aka kai ranar Lahadi, an tayar da wani gurnetin a wata babbar kasuwar canjin kudi ta Sarai Shahzada, kafin daga baya a kai na masallacin.

A fadar sashen gaggawa na asibiti, sun ce mutum 1 ya mutu, 59 sun jikkata.

Ministan harkokin cikin gida na gwamnatin Taliban, tace harin kasuwar barayi ne da ke son su yi fashi, amma kuma harin masallacin Pul-e-Khisti din , har yanzu ba’a san dalilin kai shi ba.

Amfi samun rikici a kasar lokacin hunturu, amma yanzu ga shi lokacin laifuka na kara kamari, a lokacin bazara.

Duk da haka, mahukuntan Taliban din suna ikirarin sun tsare kasar, tun bayan da suka dawo mulkin kasar, a watan Agustan shekarar da ta gabata.

Amma kuma, Hukumomin kasashen waje da masu sharhin alamuran yau da kullum, suna karyata ikirarin mahukuntan Taliban din, inda su kan ce, har yanzu da akwai rigingimun yan tada kayar baya gami da yan ta’addan ISIS da suke ikirarin kai manyan hara-hare.

Bugu da kari, barazanar yan kungiyar ISIS, da wadansu kungiyoyin ta’addanci, musamman wadanda masu kiyayya ga mahukuntan Taliban, da kuma jami’an tsaron hambararriyar gwamnati, duk suna taka rawa wajen zamewa gwamnatin Taliban ciwon kai a harkar matsalar tsaro.

Allahu Akbar: Bayan shekaru 88, za a yi sallar Taraweehi a masallacin Hagia Sophia

Labari mai dadi na isowa daga babban masallacin Hagia Sophia da ke kasarTurkiyya a birnin Istanbul, wanda ya dawo da matsayinsa na masallaci shekaru biyu kacal da suka wuce.

Kamfanin dillancin labaran Anadolu ya labarta cewa, babban masallacin Hagia Sophia na shirin gudanar da sallar tarawihi na farko a cikin watan azumin Ramadan na bana, bayan shafe shekaru 88 ana amfani da shi a matsayin gidan tarihi.

Bayan shafe shekaru mai tsayi masallacin zai dawo da ayyukan ibada a watan Ramadan Bana

Ba wai sallar tarawihi kadai ba, an ruwaito cewa, masallacin Hagia Sophia ya kuma shirya gudanar da taruka da dama na watan Ramadan kuma ana sa ran masu ibada da yawa za su ziyarci wurin a cikin wannan wata mai alfarma.

Masallacin a baya ya kasance gidan adana kayan tarihi

Masallacin Hagia Sophia a baya ya kasance a matsayin gidan tarihi ne tun shekarar 1934. Amma, a shekarar 2020 ya dawo da babbar martaba a matsayin masallaci kuma an bude shine domin musulmi su gudanar da ibada a shekarar 2020.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe