23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Kungiyar kwadago ta kasa ta ba Gwamnatin tarayya kwana 21 ta sasanta da ASUU da SSANU

LabaraiKungiyar kwadago ta kasa ta ba Gwamnatin tarayya kwana 21 ta sasanta da ASUU da SSANU

Kungiyar kwadago ta tarayya (NLC) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya akan kawo matsaya ga yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’in, ASUU, Kungiyar Ma’aikatan jami’o’i Marasa koyarwa, NASU, Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya, SSANU da ta Kungiyar Malaman Fasaha ta kasa, NAAT suke yi.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta yi gaggawar samar da kwamitin da za ta zauna da su don kawo matsaya cikin kwanaki 21,The Nation ta ruwaito.

asuuu
Kungiyar kwadago ta kasa ta ba Gwamnatin tarayya kwana 21 ta sasanta da ASUU da SSANU

Ta bayyana hakan ne ta wata takarda wacce shugabanta, Kwamared Ayuba Wabba da babban Sakataren Kungiyar, Kwamared Emmanuel Ugboaja suka sanya hannu bayan kammala wani taro.

Kungiyar ta ce zata shirya wani taro na musamman da kwamitin ayyuka (CWC) na kungiyoyin don NLC ta san matakin gaba da za ta dauka.

ASUU: Babu gudu babu ja da baya sai mun tafi yajin aiki

  • A ranar Talata ne kungiyoyin SSANU da NASU suka bayyana kudirinsu na tafiya yajin aiki daga ranar Juma’a, 5 ga watan Fabrairu
  • Kamar yadda shugaban SSANU, Mohammed Haruna Ibrahim da sakataren NASU, suka tabbatar, za su tafi yajin aikin babu gudu babu ja da baya
  • Sun bayyana wa manema labarai hakan ne bayan wata ganawar sirri ta sa’o’i 4 da suka yi da ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige

Kungiyar hadaka ta SSANU da NASU a ranar Talata suka amince da tafiya yajin aiki sai baba ta gani tun daga ranar Juma’a, 5 ga watan Fabrairu.

Shugaban SSANU, Mohammed Haruna Ibrahim da sakataren NASU, Peters Adeyemi sun bayyana wa manema labarai hakan a Abuja bayan sun yi wata tattaunawar sirri ta sa’o’i hudu da wakilin gwamnatin tarayya ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige.

Yayin sanar da manema labarai halin da ake, Adeyemi yace a matsayinsu na shugabannin kungiyar ba su da damar dakatar da ‘yan kungiyar saboda bukatarsu akan rashin adalcin da aka yi musu na raba N40,000,000,000 ba tare da an basu ko sisi ba.

Sauran dalilansu na tafiya yajin aikin sun hada da kin tabbatuwar biyansu ta IPPIS, gwamnati ta yi jinkirin daidaitawa da NASU da SSANU tun 2009, kin biyan ma’aikatan da suka yi murabus da sauransu.

Sakataren NASU yace: “Ba mu tilasta sai an tattauana damu akan janye yajin aiki ba. Mun umarci ‘yan kungiyarmu da su jajirce har sai an yi mana abinda muke so.

“Muna son gwamnati ta bamu isasshen lokacin da zamu tattauna da ‘yan kungiyarmu don mu ji abubuwan da suke so.

“Har yanzu ba mu kammala sanin abubuwan da muke bukata ba, akwai sauran matsalolin da bamu gama tattaunawa akansu ba. Za mu cigaba da jin ta bakin ‘yan kungiyar mu kafin mu tattara korafinmu mu gabatar dasu gabadaya ga gwamnati.”

A bangaren ministan kwadago kuwa cewa yayi za su yi iyakar kokarinsu wurin tabbatar da an daidaita dasu an cimma gaci.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe