24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Wasu manyan mutane da ake ganin mutuncinsu ne ke daukar nauyin ta’addanci da kashe-kashe, Gwamna Matawalle

LabaraiWasu manyan mutane da ake ganin mutuncinsu ne ke daukar nauyin ta’addanci da kashe-kashe, Gwamna Matawalle

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya zargi manyan mutanen da ake ganin mutuncinsu da daukar nauyin ‘yan ta’adda a jiharsa.

Jihar Zamfara ta dade tana fama da kashe-kashe da ta’addanci iri-iri cikin shekarun nan, LIB ta ruwaito.

Wasu manyan mutane da ake ganin mutuncinsu ne ke daukar nauyin ta’addanci da kashe-kashe, Gwamna Matawalle
Wasu manyan mutane da ake ganin mutuncinsu ne ke daukar nauyin ta’addanci da kashe-kashe, Gwamna Matawalle

A ranar Talata, 12 ga watan Afirilu, ‘yan bindiga sun kai farmaki dakunan kwanan dalibai mata na kwalejin lafiya ta kimiyya da fasaha da ke Tsafe cikin Jihar Zamfara.

Yayin tsokaci dangane da lamarin, gwana Matawalle ya ce akwai manyan mutanen da ke daukar nauyinsu.

Ya yi zargin sun dauki nauyin wasu daga cikin mazauna yankin wadanda ke kai labari ga ‘yan bindiga.

Zailani Bappa, hadiminsa na harkar watsa labarai ya yanko daidai inda gwamnan ya ke cewa:

“Alamu sun nuna cewa an dauki nauyin ta’addanci a jihar nan, manyan mutanen jihar ne suke da alhakin wannan aika-aikar. Mutane ne da ake ganin mutuncinsu.

“Kuma a cikin mutanen yankin akwai wadanda suke samun makudan kudi idan sun kai labari ga ‘yan bindiga.”

Matawalle ya ce hakan yasa ake bukatar duk masu matsayi na siyasa su rantse da Al-Qur’ani kafin su fara aiki a ofisoshinsu.

Sannan ya kula da yadda wasu manyan ‘yan siyasa suke kin amincewa da rantsuwa da Al-Qur’anin.

Ana sakin ‘yan bindiga ba tare da hukuncin kotu ba: Matawalle ya ankarar da jama’a

Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara, ya ce wani bangare na abin da ya sa ake ci gaba da fuskantar ta’addancin ‘yan bindiga shi ne rashin hukunta wadanda aka kama.

Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara, ya ce wani bangare na abin da ya sa ake ci gaba da yin ta’addanci shi ne rashin hukunta wadanda aka kama, inda ya ce sau tari ana sakin ‘yan bindiga ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu ba.

Matawalle ya bayyana haka ne a ranar Laraba a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar gwamnatin tarayya da suka kai ziyarar jaje a jihar kan hare-haren baya-bayan nan da aka kai wasu al’ummomi a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum na jihar.

Mambobin tawagar wanda Ministan Tsaro, Manjo-Janar Bashir Salihi Magashi (rtd) ya jagoranta, sun hada da mai baiwa kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo-Janar Babagana Munguno (rtd), Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Baba Alkali.

Sauran sun hada da ministan harkokin ‘yan sanda Alhaji Maigari Dingyadi, ministar harkokin jin kai da kula da walwalar ‘yan kasa, Sadiya Umar Farouk, da mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara ta musamman kan harkokin yada labarai Garba Shehu.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe