27.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Iyayen Fati Muhammad ne suka raba mu, Tsohon mijin Jarumar, Sani Mai Iska

LabaraiKannywoodIyayen Fati Muhammad ne suka raba mu, Tsohon mijin Jarumar, Sani Mai Iska

Sani Musa Haladu wanda aka fi sani da Sani Mai Iska, tsohon mijin tsohuwar jaruma Fati Muhammad wacce tauraronta ya haska a shekarun baya da suka shude ya bayyana silar rabuwar aurensu.

A wata tattaunawa da BBC Hausa ta yi da shi cikin shirinta na Daga Bakin Mai Ita, ya yi bayani akan alakarsa da tsohuwar matarsa tun daga haduwarsu har rabuwar.

sani mai air
Iyayen Fati Muhammad ne suka raba mu, Tsohon mijin Jarumar, Sani Mai Iska

Ya fara da gabatar da kansa inda ya ce an haife shi a garin Kano a Unguwar Gwammaja. Kuma ya fara ne da karatun addinin musulunci.

Ya bayyana yadda ta fara harkar fina-finai inda ya ce yana da abokai masu wasannin al’adun gargajiya kuma ya fara fim a 1998.

A cewarsa, ba Fati Muhammad kadai ya aura ba, ya taba auren wata jaruma Wasila, amma yanzu ta rasu kuma suna da diya daya da ita.

Ya ce sun kulla alakar aure da Fati Muhammad tun daga wani fim da suka tafi mai suna Sakamako, kuma ta bar sarkoki da sauran muhimman abubuwa a hannunsa. Da ga nan suka fara soyayya.

A cewarsa Marigayiya Hajiya Amina ce ta karfafa alakar soyayyar tasu. Sannan Ali Nuhu ma ya yi kokari sosai akan aurensu.

Yayin da aka tambayeshi batun tafiyarsu Ingila tare da Fati Muhammad, ya kada baki ya ce:

“Shekara ta 2002, lokacin za ayi World Cup, sai DFID da USAID, suka zo za su yi tallace-tallace da wayar da kai akan HIV/AIDS sai suka zabi kudu da arewa.

“Sai ya zama a arewa sunan Fati Muhammad ne ya fito kuma lokacin mun yi aure da ‘yan watanni. Sai aka same ni aka yi min magana akan cewa za ayi tallar kuma ba a Najeriya za ayi ba, ko dai a Afirka ta kudu ko kuma UK, shi ne silar tafiyarmu.”

Ya ci gaba da cewa kwana 7 kadai suka yi, daga baya ya koma saboda wasu dalilai. Daga baya ya bukaci ta bi shi kuma ta bi shi wanda suka kwashe shekaru 3 daga baya suka samu matsala.

Da aka tambaye shi dalilin rabuwarsu ya ce:

“Gaskiya tana da gaskiya ina da gaskiya. Saboda dalilinta a lokacin mahaifiyarta da mahaifinta, Allah ya ji kan su don duk yanzu sun rasu.

“Ni kuma dalilina a lokacin ban gama senior Secondary School ba na samu dama ba zan so in saki ba don na yi nisa. Ita kuma tana matukar kaunar mahaifiyarta.”

Ya daga nan ne suka nemi rabuwa wacce sai da suka dawo Najeriya sannan ya yi mata saki daya, sai dai ita ta ce saki uku ne kuma a haka suka tafi.

Da aka tambayeshi idan zai yiwu ya mayar da ita ya ce ai ba zai yiwu ba saboda a wurinta saki uku ne. Amma a cewarsa kaddara ce kawai ta raba su.

Yadda tsohon mijin Momi Gombe zai yi wufff da Nana Izzar so, abokiyar sana’arta

Cikin kwanakin nan hotuna su ka bayyana na wani fitaccen mawakin Kannywood, Adam M Fasaha, wanda tsohon miji ne ga Jaruma Momi Gombe da wata jarumar ta daban, Minal Ahmad wacce ta fito a matsayin Nana cikin shirin Izzar so mai dogon zango.
Shirin Izzar so ya sa ta yi matukar farin jini da shahara inda tun daga nan ta samu karbuwa a masana’antar Kannywood don akwai sababin shirye-shirye kamar ‘Sarki Goma’ da sauransu da ta taka babbar rawa a cikin su

Hotunan nata tare da mawaki Adam sun yi matukar daukar idanu don mutane da dama sun yi mamakin yadda zai yi wuff da abokiyar aikin tsohuwar matarsa.
Minal ta kasance bakar mace mai tsananin kyau da diri irin na mata, hakan ya ke sawa masoyanta su ke matukar nuna mata kauna.
Duk da dai akwai alamun cewa Momi Gombe kawar Minal ce don masu bibiyarsu a kafafen sadarwa zasu dinga ganin su na hawa kan wakoki daban-daban a tare.
Shin ko wannan auren zai zama cikas ga kawancensu?

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe