34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Matashi ya sha alwashin ciyar da amala, nama, tsire da giya kyauta idan ya zama shugaban ƙasar Najeriya

LabaraiMatashi ya sha alwashin ciyar da amala, nama, tsire da giya kyauta idan ya zama shugaban ƙasar Najeriya

A yayin da ‘yan siyasar Najeriya ke ci gaba da bayyana muradin su na tsayawa takarar shugabancin ƙasar a shekarar 2023, wani matashi dan Najeriya mai suna Ayo FBI a shafin twitter ya sa da yawa daga cikin mabiyansa dariya da irin nasa salon idan aka zabe shi a matsayin shugaban ƙasar.

A cewarsa, ta hanyar amfani da karin maganar Yarbawa, ya ce al’amura za su yi aiki yadda ya kamata a lokacin da zai shugabanci ƙasar. Ayo wanda ya bayyana hakan a wani rubutu mai ban dariya ya rubuta: Wani matashin Najeriya ya bayyana cewa yana son maye gurbin Buhari.

Amalaa
Matashi ya sha alwashin ciyar da amala, nama, tsire da giya kyauta idan ya zama shugaban ƙasar Najeriya

“Cikin tawali’u da gagarumin goyon bayan Ubangiji Madaukakin Sarki da na ku baki ɗaya, ina bayyana aniya ta tsayawa takara mafi girma a ƙasar nan, wato ofishin Shugaban Tarayyar Najeriya”.

“A lokacin da nake Shugaban Najeriya, ɓera zai yi kuka kamar Ɓera, Tsuntsaye za su yi ihu kamar tsuntsu, dan Adam zai yi kama da mutum” .

  • Tsire zai zama kyauta ga kowa
  • Amala da naman Akuya za ta zama abinci ga dukkan ‘yan Najeriya.
  • ‘Yan Najeriya ba za su ƙara biyan kudin abinci ba. Abinci kyauta ga kowa.
  • Babu wani dan jam’iyyata da ya zaɓe ni da zai sake biyan kuɗin barasa. Kamfanonin barasa na Najeriya za a ba su izinin yin giya don kyauta musamman ga duk waɗanda suka zaɓeni. A martanin da suka mayar, wasu daga cikin mabiyansa da suka ji dadin batunsa sun ce an fara aikin yaƙin neman zaɓen da gaske.

AbdulMuiz ya rubuta cewa: “Babu lokaci, mu shirya taron da karfe 12 na dare domin tattauna tsare-tsare da dabarun mu na ratsa yankunan karkara, kasuwannin da za mu ziyarta, gidajen marayun da za su kai kayayyaki da kuma zaɓar masu shara da doka da za su yi taho-mu-gama da mutane, 2023 mai tsarki ne.”

Matashi ya hallaka budurwar sa ,ya kwanta da gawarta na kwanaki 6 bisa umurnin boka

An damke wani mutum mai suna Ifeanyi Njoku matashin an kama sa ne da laifin kashe budurwarsa mai suna Precious Okeke ‘yar shekara 24 a wani gida da ke Badore a yankin Ajah a jihar Legas.

PUNCH Metro ta tattaro cewa masoyan suna zama ne titin Oke, unguwar inda Njoku ya hallaka budurwar tasa domin yin tsafi.

Wakilin Punch Metro ya samu labarin cewa akwai wata matsafiya da ke taimaka wa wanda ake zargin, wacce ta umurce shi da ya yi lalata da gawar budurwar ta sa.

Abinda Njoku ya yi abune haramtacce wanda ya shafe tsawon kwanaki shida yana kwana da gawa, warin da ke fitowa daga gidan da yake shine ya fargar da makwabta suka sanar da mahukuntan gidan.
Wata shaidar gani da Ido mai suna Elizabeth tace an gano gawar Okeke ne a yayin da ake bincike.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe