24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Kyawawan ‘yan uku sun fada soyayyar saurayi 1 kuma sun shirya amarcewa da shi

LabaraiKyawawan 'yan uku sun fada soyayyar saurayi 1 kuma sun shirya amarcewa da shi
aa0887e8fd25bd64
Kyawawan ‘yan uku sun fada soyayyar saurayi 1 kuma sun shirya amarcewa da shi

Kwanakin baya kadan aka sami labarin wasu ‘yan biyu mata zasu amarce da mutm daya hakan ba karamin mamaki ya baiwa mutane ba,Sai kuma gashi yanzu an sake samun wani labari makamancin sai inda wasu ’yan uku mata ‘yan kasar Kenya suma suka lalubo nasu angon in da suna gab da amarcewa da miji daya. Labarin Eve, Mary da Cate labarine mai ban sha’awa da al’ajabi. ‘Yan uku ne da suka kasance masu kamanni daya hatta da burin su da bukatun su ya kasance ɗaya. ‘Yan uku sun bayyana cewa suna soyayya ne da saurayi daya wanda hakan ya faru ne a lokuta daban-daban.

Baya nuna banbanci a tsakanin mu

Da yake labartawa wata amintacciyar kafar yada labarai ta kasar Kenya Tuko, yace soyayyar su soyayya ce da ke cike da farin ciki domin yana basu kulawa iri daya babu banbanci.

Yadda muka fara soyayya da shi

Mary ta labarta cewa Cate ce ta fara haduwa da abin ƙaunar su,kuma batayi kasa a gwiwa ba ta shafa musu labarin, suma kuma nan take su ka bayyana sha’awar su akan shi .
“Cate ce ta fara haduwa da shi tazo ta bamu labari muma kuma nan take Allah ya jarabce mu da son shi” in ji Mary.

Muna fita yawon shakatawa a lokuta mabanbanta

Mary ta kara da cewa duk da sun kasance suna harkaloli daban daban hakan bai hanasu samin lokacin shakatawa da masoyin na su ba.
“Mun kasance muna da ayyukan yi wanda ya sanya muka tsara haduwa da shi sau daya a kowani karshen mako.
Haduwa ta dashi yakan kasance ranar Litinin, Eve a ranar Talata sai Cate a ranar Laraba,” in ji marya.

‘Yan matan kara bayyana yadda suka shafe tsawon shekara daya da rabi suna soyayya wanda a yanzu haka suna kan shirye-shiryen aure.

So makaho ne: Matashi mai shekaru 25 ya daura dammarar yin wuff da tsohuwa mai shekaru 85

Ba tare da dubi da tazarar shekaru 60 din da ke tsakaninsu ba, wani matashi ɗan shekara 25 ya faɗa kogin son wata tsohuwa mai shekaru 85 mai suna Thereza.

Masoyan biyu, Thereza da Muyiwa sun shirya rayuwar aure duk da ƴaƴan masoyiyarsa da abokansa sun nuna rashin amincewarsu.
Muyiwa ya bayyana wa Afrimax a wata tattaunawar da suka yi yadda ya bar ƙasarsa ta Congo don karatu a jami’a inda ya kama gidan hayan Thereza tare da abokinsa.

Saurayin ya ce, a baya ya yi soyayya da ƴan mata bai jidaɗi ba, amma Thereza ta bambanta da sauran mata, sannan yana tsoron kada ta mutu da wuri.
Ya ce tana kyautata masa

Kamar yadda ya shaida:

“Ina tuna ranar wata Juma’a sanda abokin zama na yayi nisan kiwo, yunwa ta kama ni, gashi bamu da abinci.

“Na galabaita kwarai. Kawai sai tsohuwar ta kawo min abinci. Yadda ta tarairaye ni ne yasa na tsunduma a kogin soyayyarta.”
Duk da tsohuwa ce wacce tayi jika dani, amma ina matukar kaunarta.”

Yayi kira ga masu sukarsa da su sakar masa mara ya yi fitsari, saboda wacce yake ƙauna, inda yace:

“Wannan ra’ayina ne, kuma shine muradi na.”

Sun kusa shigewa daga ciki

Thereza ta bayyana tsananin ƙaunar da take wa Muyiwa kamar yadda shima yake sonta. Ta ce a shirye take da tayi wuff dashi.

A cewarta:Shekaru na 85. Ina da ƴaƴa 8 da jikoki 20. Idan za’ayi dubi da shekarun saurayi na, kusan sa’an jikana na biyar ne. Amma muna ƙaunar juna. A shirye nake da in zama matarsa.”

Ga wasu daga cikin tsokacin ƴan Najeriya

Abdurrahman Ahmad ya ce:

“Shegiya duniya ya ga naira yana jiran Allah ya kar giwa ƙasa, ya samu yarinya mai jini a jika yayi wuff da ita.”

Khaleepha M Salees Sumaila ya ce:
Ba ta yi tsufa ba tunda tana da kudi, a wannan yanayin kowa ya samu wannan damar ba zai yi wasa da ita ba, duk kuma wanda ya kushe wa wannan matashin to hassada yake masa.”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe