24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Mutum 28 sun rasu a wani mummunan haɗarin jirgin ruwa a Sokoto

LabaraiMutum 28 sun rasu a wani mummunan haɗarin jirgin ruwa a Sokoto

Aƙalla mutum 28 ne su ka nutse a wani haɗarin jirgin ruwa a ƙauyen Gidan-Magana, cikin ƙaramar hukumar Shagari a jihar Sokoto. Jaridar Punch ta rahoto

Dagacin ƙauyen, Mohammed Auwalu, ya bayyana cewa haɗarin ya auku ne a ranar Laraba, yayin da matafiyan su ke tsallaka rafin a jirgin ruwan domin zuwa ƙauyen Badiyawa mai maƙwabtaka da su.

An bayyana yadda lamarin ya auku

Auwalu ya bayyana cewa haɗarin ya auku ne lokacin da jirgin ruwan ya daki wata bishiya a cikin ruwan sannan ya kife.

A cewar Auwalu, jirgin ruwan yana ɗauke da mutum 34, da yawa daga cikin su mata da ƙananan yara.

Lokacin da ya daki bishiyar sannan ya kife a cikin ruwan, mutum 6 kawai aka ceto, yayin da aka ciro gawarwarki 28.

Matafiyan su mutum 34 ne, suna tafiya ne zuwa ƙauyen Badiyawa a jirgin ruwan yau da safe (Laraba), suna cikin tafiya jirgin ya daki wata bishiya sannan ya kife.

Masu ceton gaggawa sun samu nasarar ceto mutum 6 a raye, yayin da aka ciro gawarwaki 28. ‘Ya’ya na guda biyar suna daga cikin waɗanda su ka rasu a haɗarin.

Baa samu jin ta bakin hukuma ba

Ƙoƙarin jin ta bakin shugaban ƙaramar hukumar Shagari, ya ci tura inda baa samu layukan wayar sa ba.

Jihar Sokoto ta fara feshin murar tsuntsaye

Gwamnatin jihar Sokoto ta fara aikin kawar da kaji daga kamuwa da cutar murar tsuntsaye (Avian Fluenza) tare da farfado da wuraren bayar da rahoton cututtuka domin magance yiwuwar ɓullar cutar a jihar, The Punch ta ruwaito.

Kwamishinan Lafiyar Dabbobi da Raya Kamun Kifi, Farfesa Abdulkadir Junaidu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Sokoto ranar Laraba.

Ya ce duk da cewa ba a samu ɓullar cutar murar tsuntsaye a jihar ba, amma rahotannin da aka samu a fadin ƙasar nan da kuma jihohin da ke maƙwabtaka da su, ya sa a ɗauki matakan da suka dace.

Jihohi 27 da kananan hukumomi 85 sun riga sun kamu da cutar a fadin tarayyar ƙasar nan a cikin ɓullar cutar guda 382 da ta kai ga halakar da tsuntsaye miliyan 1.8.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe