29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Bidiyon wani makaho mai bara yana ƙin amsar sadakar matattun kuɗi ya jawo cece-kuce

LabaraiBidiyon wani makaho mai bara yana ƙin amsar sadakar matattun kuɗi ya jawo cece-kuce

Bidiyon wani makaho mabaraci yana ƙin amsar kuɗin da wata mace fasinja ta bashi ya ɗauki hankulan mutane da dama.

A cikin bidiyon wanda @saintavenue_ent1 su ka wallafa a shafin Instagram, makahon ɗan jihar Akwa Ibom, wanda ya ke tare da ɗan jagorar sa, yayi wa macen fasinjar keke Napep tsiya saboda ta bashi kuɗi marasa kyau.

Makahon wanda yayi magana a cikin yaren sa a bidiyon, ya bayyana cewa ya gane kuɗin ba su da kyau bisa taimakon ɗan jagorar sa.

Daga nan sai ya jefar da kuɗin cikin keke Napep ɗin, wanda hakan ya fusata wacce ta bashi matattun kuɗin da farko.

Budurwar ta fusata da makahon

Budurwar ta caccaki makahon bisa ƙin amsar kuɗin da yayi inda ta ke tuhumar ta ya akai ya san kuɗin ba su da kyau duk da cewa yana makaho, alamun cewa ta manta da bayanin da yayi da farko.

Ku kalla bidiyo anan

Mutane sun tofa albarkacin bakin su

@miss_social20 ya ce:

Duk da dai mun san cewa akwai ‘yan damfara sosai a cikin su, abinda budurwar ta yi ba ta kyauta ba, ya bayyana cewa ɗan jagorar sa ya faɗa masa, abinda abokina ɗan Akwa Ibom ya fassara min kenan.

@bestybesst ya ce:

Yaji a jikinsa, suna da baiwar taɓa abu, meyasa za ki ba makaho kuɗi marasa kyau

@citycoluss ya ce:

Abinda budurwar ta yi bai dace ba. Makahon yaji cewa kuɗin ba su da kyau. Kuɗin sun yage fa. Sannan abinda za tayi kawai shine ta ɗauki bidiyon sa ta yaɗa a yanar gizo. Kyauta mara kyau ba abu mai kyau ba ne.

Anata cece-kuce akan rawan barar da mutuncin da Jarumi Tahir Fagge ya yi a wani gidan rawa da wata budurwa

Fitaccen jarumin masana’antar Kannywood, Tahir Fagge wanda ya fi bayyana a matsayin uba a fina-finai yana shan caccaka bayan wani bidiyonsa yana tikar rawa tare da wata budurwa ya bazu a kafafen sada zumunta.

Bidiyon nasa ya janyo mutane suna ta maganganu marasa kyau akan masa’antar har wasu suna ganin bai dace dattijo irinshi ya yi irin wannan rawar ba, Masarauta Entertainment ta Youtube ta ruwaito.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe