27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Zukekiyar budurwa ta’tashi’saurayi ta hannun abokan sa,ya aure ta babu bata lokaci

LabaraiZukekiyar budurwa ta'tashi'saurayi ta hannun abokan sa,ya aure ta babu bata lokaci
8a66238d3e0b5163

Wata budurwa ta kasa boye muradin ta wanda hakan yayi silar auren ta

Wata ‘yar Najeriya da tayi arangama da hoton wani kyakyawan mutum a wani statues,ganin hoton ya sa ta kwallafa ranta a kan sa abu kamar wasa har takai ga maganar aure. Haduwar su ta kasance haduwa mai ban mamaki inda basu taba ganin juna ba amma soyayya ta kullu a tsakanin su.ko da ganin hoton sa Sai ta aika masa da sako ta hannun wani abokin sa.

Ta aika masa da sako inda ta bayyana sirrin zuciyar ta

Sakon da ta aika ya kasance dan gajeren sako, ‘yan kalmomin basu gaza layi dayaba amma ya yi sanadiyar soyayyar su.
Abin da sakon ta yakun sa:‘Ka gaya masa ina son sa zan aure sa. Duk abinda ya baka ansa ka gayamin.” Wanda aka aikawa da saƙon ya maida abin wasa har da yar dariyar sa,amma abin mamaki karamar magana ta zama babba inda ta fito shafin twitter ta bayyana wa duniya yadda lamarin yafaru.
Kadan daga cikin martani masu amfani da shafin yanar gizo:
@Pharm_chocolate ya ce: “Mata kin wasa wukar ki fa! Ina taya ku murna.”
@Nickib900 ya ce: “Ina tayaka murna irin samarin yanzu girman kai idan ka yi magana omo na forming woo.”
@Xtopher_Uzo ya ce: “Mata kun gani? Ta mutu? Duniya ta ƙare?
@KUNLEADEIGBE ya ce: “Haka za a yi….. no yeye green light. Ba kunya fitar da abinda ke ranki.

Mata ku koyi kulawa da jiki: Namijin da ya fara daukar ciki a duniya ya koma cakaras bayan haihuwa ta 3
Ko kun taba jin labarin mutum na farko a duniya da ya taba daukar juna biyu?

Duk da bai yi kama da maganar da hankali zai dauka ba, amma da gaske ne, Legitnaijanews.com ta ruwaito.
A cewar wani mutum mai suna Thomas an haifesa a mace, amma tuntuni yasan da cewa ya so zama namiji, saboda haka yana da shekaru 20, ya fara allurar testosterone (sinadin kwayoyin halittar maza), wanda ya yi sanadiyyar bayyanar sajensa, kankantar masa da murya da rage masa mazantaka.

A shekarar 2012, ya yanke shawarar yanke nonuwansa, yayin da matarsa ta cire mahaifarta.
Amma a wannan lokacin, Thomas ya yanke shawarar barin al’aurarsa ta mata.
Duk da ta hanyar dashe aka sanya masa ‘da. Amma a halin yanzu yana warkewa bayan ya haifi ‘ya’ya uku.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe