24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Matashi ya hallaka budurwar sa ,ya kwanta da gawarta na kwanaki 6 bisa umurnin boka

LabaraiMatashi ya hallaka budurwar sa ,ya kwanta da gawarta na kwanaki 6 bisa umurnin boka
youth kills n punished
Matashi ya hallaka budurwar sa ,ya kwanta da gawarta na kwanaki 6 bisa umurnin boka

An damke wani mutum mai suna Ifeanyi Njoku matashin an kama sa ne da laifin kashe budurwarsa mai suna Precious Okeke ‘yar shekara 24 a wani gida da ke Badore a yankin Ajah a jihar Legas.

Ya hallaka budurwar tasa don yin tsafi da gawar ta sa

PUNCH Metro ta tattaro cewa masoyan suna zama ne titin Oke, unguwar inda Njoku ya hallaka budurwar tasa domin yin tsafi.

Wakilin Punch Metro ya samu labarin cewa akwai wata matsafiya da ke taimaka wa wanda ake zargin, wacce ta umurce shi da ya yi lalata da gawar budurwar ta sa.

Abinda Njoku ya yi abune haramtacce wanda ya shafe tsawon kwanaki shida yana kwana da gawa, warin da ke fitowa daga gidan da yake shine ya fargar da makwabta suka sanar da mahukuntan gidan.
Wata shaidar gani da Ido mai suna Elizabeth tace an gano gawar Okeke ne a yayin da ake bincike.

Shaidar gani da ido ta labartawa jami’an tsaro yadda abin yafaru

Ta ce, “Yaron ya hallaka budurwar tasa ne kimanin kwanaki shida da suka wuce, inda ya bayyana cewa ya kashe ta ne don ya yi tsafi da gawar don ya sami kudi. Ya ce an bashi umurnin cewa ya yi jima’i da gawar budurwarsa har na tsawon kwanaki bakwai,cikin rashin sa’a aka damke shi a rana ta shida.

Warin gawar shine abu na farko da ya fara addabar makwabtan dake kusa da su. Hakan ne yasa, makwabtan suka kai korafi ga mahukunta gida domin sanin meke faruwa inda a yayin bincike ne aka gano gawar Precious.
“Nan take aka damke Ifeanyi inda aka kai shi ofishin ‘yan sanda na Lamgbasa kuma ya amsa laifin sa a yayin da ake yi masa tambayoyi ya amsa cewa shi ya kashe budurwar tasa kwanaki shida da suka wuce.

Majiyar ta bayyana cewa Ifeanyi ya yi yunkurin bayar da Miliyan 6 domin ganin kawai an kashe maganar; An kuma samu labarin cewa ya dauko budurwar ta sa ne daga kauye inda suka tare a wannan gidan.”

Jami’an tsaro sun bada shaidar faruwar lamarin

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa mamacin da wanda ake zargin ya kashe ta sun kasance masoya ne.

Ya ce, “An kama mutane biyu da ake zargi akan lamarin Ifeanyi Njoku da Mbam Atunmufor mai kimanin shekaru 36. An damka su zuwa sashin binciken manyan laifuka da leken asiri yankin, Yaba, domin ci gaba da bincike.”

Baturiyar da ta halaka saurayinta dan Najeriya a kasarsu ta ci gaba da walwalarta, har da zuwa mashaya
An ga wata baturiya da ta halaka saurayinta dan Najeriya ta hanyar daba masa makami a mashaya tana shan giya tare da mahaifinta, yayin da dangin wanda ta halakan suke zaman makoki, LIB ta ruwaito.

Courtney Tailor Clenney ta halaka Christian Toby Obumseli, dan Najeriya sannan mazaunin Amurka ta hanyar daba masa wuka a ranar Lahadi, 3 ga watan Afirilu, a mazauninsu dake Miami.
Anyi ram da Courtney, amma sai tayi barazanar halaka kanta, hakan yasa ‘yan sanda suka mikata ga asibitin mahaukata karkashin dokar Baker.

A Florida, jami’an tsaro na da damar mika mutum asibitin mahaukata na tsawon kwanaki uku ta hanyar amfani da dokar kasa ta Baker.

Babu wanda ya tuhumi Courtney, kuma tana rayuwarta lakadam.

An ganta a mashaya tare da mahaifinta a daren Juma’a, 8 ga watan Afirilu, sai dai wata mata ‘yar Najeriya, Nnenna da ta ganta ta fatattaketa daga mashayar.
“Eh, ki tafi. Ki tafi, saboda kin halaka saurayinki,” An jiwo Nnenna na fadawa Courtney.

An take Courtney da mahaifinta suka bar mashayar.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe