24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Wani magidanci ya lakaɗawa matarsa duka saboda abincin Sahur

LabaraiWani magidanci ya lakaɗawa matarsa duka saboda abincin Sahur

Wani magidanci mai suna Taofeek Gbolagade, a ranar Talata, ya lakaɗawa matarsa mai ɗauke da juna biyu dukan tsiya, saboda ba ta haɗa masa abincin Azumi ba.

Legit.ng ta rahoto cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 4 na dare a gidan su dake a rukunin gidaje na Ogbere, Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

An bayyana yadda lamarin ya auku

A cewar shaidun gani da ido, mutumin yana da ɗabi’ar dukan matar sa a duk lokacin da su ka samu saɓani.

Shaidar ya bayyana cewa:

Magidancin yana dukan matar sa duk lokacin da su ka samu ƙaramin saɓani. Na samu na ɗauki abinda ya faru yau. Musulmi ne, ina tunanin sun samu saɓani ne akan abincin Sahur.

Magidancin bai damu da cewa tana ɗauke da cikin ɗan sa na biyu ba, ya cigaba da dukan ta. Ta yi ta ihu sannan daga bisani ta samu ta gudu zuwa gidan iyayen ta. Gbolagade ya tsere daga gidan sa bayan ‘yan sanda sun bada sanarwar neman sa ruwa a jallo.

Ana gudanar da bincike kan lamarin

Da ake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin hukumar ‘yan sanda na jihar Oyo, Adewale Osifeso, ta bayyana cewa tuni aka fara gudanar da bincike akan lamarin.

Bidiyon wata mata yayin da take gwangwaje mijin ta da mota mai kimar N87m ya dauki hankula

Wata mata mai ɗauke da juna biyu wacce ake sa ran haihuwarta kwanan nan, sannan ta wuce hutun bangali na al’ada ta yi wa mijin ta kyautar mota ƙirar Lamborghini Huracan Evo wacce ta kai zunzurutun kuɗi har miliyan 87 (N87m)

Mijin zai cigaba da ɗawainiya

A lokacin da Anes Ayuni Osmanis, 19, za ta haihu cikin wannan watan, mijin ta Weldan Zulkefli shine zai cigaba da kulawa da jaririn ta yadda matar sa za ta murmure. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Wannan al’ada ce kuma hutun na bayan haihuwa yana ɗaukar kwanaki ɗari. A cikin waɗannan kwanakin mijin shine zai cigaba da kula da lamura.

A matsayin kyautar sadaukarwar da Zulkefli zai yi a cikin kwanaki ɗarin hutun da matar sa za ta yi, matar sa ta yi masa wata gagarumar kyautar bazata. Ta miƙa masa mota cikin shaukin ƙauna a cikin wani bidiyo da aka wallafa a Tiktok.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe