Dangane da shiri mai dogon zango na Alaqa wanda ya dauki hankalin jama’a da dama a makon nan bayan ganin an sauya jaruma wacce tauraronta ya fara haskawa, Habiba Y Aliyu wacce aka fi sani Ummi Alaqa ya bata wa masu kallo rai, Ali Nuhu ya magantu.
Mutane sun dinga surutai akan sauya jarumar inda wasu suke ganin saboda Maryam Yahaya ta fi ta fada ne a kamfanin yayin da wasu ke ganin kamar bakin ciki ake yi wa jarumar shiyasa aka cire ta aka mayar da Maryam.

Mutane da dama sun dinga surutai kowa yana tofa albarkacin bakinsa. Bayan ganin hakan ne yasa Tashar Tsakar Gida ta yi tattaki don samun mai shirya shirin kuma mai bayar da umarnin shirin, Ali Nuhu don jin albarkacin bakinsa.
Jarumi Ali Nuhu ya amsa tambayoyin da aka yi masa dangane da cire jarumar. Ya bayyana cewa yana da kwakkwaran dalilinsa na cire jarumar wanda hakan ne zai fi zama masa alkhairi, da jarumar da ma kamfanin gaba daya.
Ali Nuhu ya ce bayyana dalilin zai iya taba mutuncinta
Ali Nuhu ya bayar da hakuri inda ya ce ba zai iya fadin dalilin ba. Amma hakan shi ne alkhairi ga kamfanin da ita kanta jarumar.
Ya ci gaba da cewa cire jarumi ko sauya sa ba al’adar kamfanin FKD Productions bane amma tunda aka ga haka akwai kwakkwaran dalilin da yasa ba za a ji daga bakinsa ba.
Tashar Tsakar Gida ta so jin ko dai rashin kunya ta yi masa ko kuma wani babban jarumi amma Ali Nuhu ya ce sam ba haka bane.
Daga karshe Ali Nuhu ya ce abinda ya faru da ita abu ne da zai taba mutuncinta wanda yana da diya kuma ba zai so hakan ya faru da ita ba, shiyasa ya yi gaggawar cire ta.
Ya ci gaba da cewa yana fatan ta ji shawararsu ta yi aure ko kuma ta dan dakata da shirin na wani lokaci kafin aga abinda hali zai yi.
Muna fatan hakan ya zama mafi alkhairi, Ameen.
Mutane na ta sanyawa Ali Nuhu albarka kan yadda ya yiwa wata mai tallar awara goma ta arziki lokacin da ta yi bari
Duk da irin suka da kahon zuka da akan kafa akan jaruman masana’antar Kannywood wani lokacin sukan yi abin da wasu daga cikin al’umma ke yaba musu gami jinjina musu da fatan su zama abin koyi ta wannan fanni.
Wadanda suka fi samun wannan yabo sun hada da Hadiza Gabon, Mansurah Isah, Ali Nuhu, Adam A Zango, Aisha Humaira da dai sauran su.
A wannan karon jarumi Ali Nuhu ne yayi wani abin arziki, inda abokin sana’arsa, Abdul Saheer, wanda aka fi sani da Malam Ali a cikin shirin “Kwna Casa’in” ya wallafa a shafinsa cewa wani abokinsa ya bashi labarin abin kirkin da yayi akan idon sa, inda ya rubuta cewa:
“Jiya nake hira da wani abokina, sai yake ce min Abdul Wallahi Ali Nuhu ya taba yin wani abu wanda ya taba ni, nake tambayarshi, mene ya faru?
Sai ya ce watarana ya ga wata yarinya mai tallar Awara tana kuka alamar tayi barin awarar ta. Sai ga Ali Nuhu ya fito yana zuwa ya ga yarinyar tana ta sharbar kuka, nan take yaje har inda yarinyar take ya tsaya yake tambayarta shin mene yake faruwa dake?
Sai ta ce awarar ta ce ta bare, sai ya ce to daina kuka kinji, ya dauri kudi masu kauri ya ce ga wannan rike na baki duka kije, amma fa ki daina kuka.
Bayan Ali Nuhu ya shiga mota ya tafi sai mutanan wajen suka ce wannan kudin da ya bawa wannan yarinyar fa yanzu yayi wani aikin “Voice Over” aka bashi kudin, ko aljihu bai saka kudin ba ya dauka ya bawa wannan yarinyar.
Abokina ya ce shifa tun daga nan ya sallamawa Ali Nuhu akan gaskiya wannan mutumin kirki ne.
Muna alfahari da kai matuka sir
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com
Kinan kusan Mutuncin Jaruma Maryam Yahaya yazube a Idan Mutane Shine kasaka dumun Bakomai ma Idan mutumcin nata ya ƙara zubiwa baƙi ɗaya.
Kekuma wannan yazama izina a wajanki da ke koma gaban iya yanki kiy Aure yafiyi mike wannan Harkar ta wasan kwaikwayo.