27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Ladan ta haifi da namiji

LabaraiKannywoodTsohuwar jarumar Kannywood, Fati Ladan ta haifi da namiji

A safiyar Litinin, 11 ga watan Afirilun 2022 da misalin karfe 8:17 na safe, Allah ya azurta tsohuwar jarumar Kannywood, Hajiya Fati Ladan da jariri namiji a wani asibitin kudi da ke Unguwar Rimi a Kaduna, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Idan ba a manta ba, Fati Ladan ta kai tsawon shekaru 4 da aure kafin ta samu haihuwa, wanda babu dadewa dahaihuwarsa Ubangiji ya dauki abinsa.

fati ladan da mijinta
Tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Ladan ta haifi da namiji

Sai kuma a ranar Talata, 21 ga watan Mayun 2019 Ubangiji ya kara azurta ta da haihuwar jaririya wacce aka rada wa Aisha, amma ana kiranta da Humaira. Yanzu haka saura kusan wata daya Aisha ta cika shekaru 3 da haihuwa.

Wani abin ban sha’awa da kuma mamaki shi ne an haifi Humaira a watan Ramadan ga shi wannan kanin nata ma Allah ya kawo shi da watan Ramadan.

Fati Ladan mata ce ga fitaccen dan gwagwarmayar nan kuma Shugaban Kungiyar Tuntubar Matasan Arewa, Alhaji Shettima Yerima.

Tsohuwar jarumar Kannywood Naja’atu Muhammad, wacce ta yi fim din Murjanatu ‘yar Baba ta haihu

Aure ya yi albarka, tsohuwar jarumar Kannywood, Naja’atu Muhammad wacce aka fi sani da Murjanatu ‘Yar Baba ta haihu yau, ranar Alhamis, 24 ga watarin Maris din shekarar 2022.

Mijinta, Abdullahi Shehu, fitaccen dan wasan kwallon kafa ne, ya wallafa hakan a shafin sa na Instagram.

Kamar yadda ya bayyana, ta haifi yaro namiji yau da safen nan kuma tana cikin koshin lafiya.

Bayan wallafar ta shi, nan da nan mutane suka fara wallafawa a shafukansu, fitatattun shafuka kamar Arewafamilyweddings ma sun wallafa.

Manyan jarumai da mawaka, kamar Ali Nuhu, Ali Jita da sauran su sun bazama wurin yi masa barka suna fatan Allah ya raya.

Kamar yadda ya wallafa da harshen turanci:

“Muna farin cikin sanar da ku cewa mun samu karuwar da namiji. Mahaifiyarsa da yaron duk suna cikin koshin lafiya. Mun gode wa Allah.

“Muna farin cikin zuwan jaririn mu yau da safe. Mun gode da addu’o’in ku.”

Tun bayan fim din da jarumar ta yi a lokacin tana karama, Murjanatu ‘Yar Baba, ta samu daukaka da kuma suna.

Mutane da dama sun yi tunanin zata ci gaba da fim idan ta girma. A baya an ga yadda take kawance da Jaruma Maryam Yahaya sosai, bayan bayyanar ta a bikin birthday din ta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe