24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Ko kallo gawar mahaifina bata isheni ba, Jaruma Kudu, Chioma Toplis

LabaraiKo kallo gawar mahaifina bata isheni ba, Jaruma Kudu, Chioma Toplis

Wata jarumar Nollywood mai suna Chioma Toplis, mai shekaru 48 ta yi alawadai da halayyar mahaifinta, wanda jogora ne a wata Coci, shafin Instablog na Facebook ya ruwaito.

Chioma Elizabeth Toplis jarumar masana’antar shirya fina-finain Najeriya ce. Ta yi fice akan sana’arta a shekarar 2004 a wani fim “Stolen Bible ” tare da wata Kate Henshaw.

topolis
Ko kallo gawar mahaifina bata isheni ba, Jaruma Kudu, Chioma Toplis

Jarumar ta bada labarin yadda ta girma tana mamakin dalilin da yasa mahaifiyarta ta auri shashashan mutum irin mahaifinta.

Ta bayyana dalilinta na daukar zafi

A cewarta:

“A zatona mu kadai ne ke da sakaran mahaifi. Shima jagora ne a Coci. Mahaifiyata ta rubu da mahaifina saboda dalilai da dama wadanda suka hada da; ragwanta, sakarci, cin amana, son kai, shashanci, duka, maganar gaskiya da duk wasu munanan dabi’u.

“Kunsan wani abu? Tayi sa’ar zama da ranta.

“Na girma ina mamakin dalilin da yasa mahaifiyarta ta auri irin wannan azzalumin mutumin.

“Bazan taba halartar bikin birnesa ba, koda kuwa ina Najeriya ballantana in kaiga kuka. Amma wani abun birgewa shi ne, babu daya daga cikin ‘yan uwana da zai yi hakan.

“Sai dai dan uwana guda daya, wanda shi ne babban ‘da, shi ma don haka al’ada da doka suka tilasta.

” Eh, dole zai rigamu mutuwa saboda yazo duniyar nan kafin mu.”

Yadda mahaifiyata ta dinga hakuri da cin zarafinta da mahaifina ya ke mata har sai da ya halakata

Akwai mata da dama da suke fuskantar cin zarafi daga mazajensu, sai dai su kan boye don gudun jama’a su san halin da suke ciki.

Wani dan Najeriya ya labarta yadda mahaifiyarsa, wacce Kirista ce ta kwarai ta yi rayuwar aure cike da cutarwa, har zuwa lokacin da mahaifinsa, wanda shugaba ne a wata Majami’a ya lakada ma ta duka har sai da ta rasa ranta, Instablog ta ruwaito.

A cewarsa:

“Hukumar Majami’a ta nada mahaifina a matsayin jagora, a ranar da na kai korafi ga wani Fasto cewa an kwantar da mahaifiyata a asibiti, saboda yadda ya nada ma ta matsanancin duka.

“Mahaifiyata ta yi mamakin jin labarin tana kwance a gadon asibiti. Yayin da matar Feston ta kai ma ta ziyara, mahaifiyata ta ce “meyasa” sai ta ce ma ta, “mijina ya ce sun ba shi mukamin ne don su samu damar sa masa ido.”

“Bayan wasu makwanni, lamarin ya sake maimaita kanshi. Mahaifina ya dawo gida ya rufe mahaifiyata da duka, saboda bata biya mana kudin makaranta ba.

“Ta ruga ta tafi neman agaji gidan faston, inda faston ya ce:

“Na yarda da Ubangiji, wannan yana daga cikin rayuwar aure, hakan na nufin daura damarar cigaba da nunawa mijinki kauna”.

“A lokacin da zata tafi, ya kirata ya karanta ma ta “Ayar psalms 91” sannan matarsa ta kara da “Ayar psalms 40”

“Da haka mahaifiyata ta dawo gida.

“Wata rana mahaifiyata ta kara guduwa gidan faston don tsare rayuwarta a ranar ne faston ya bata wadannan dokakin. Ki yi azumi na kwana 21, duk abunda ya faru cikin kwanaki 21, kada ya razanaki, ki karanta ayar psalms 91.

“Ki amshi wannan man tsarin ki yayyafa a kayan mijinki sannan ki karanta ayar psalm ta 40, bayan kin gama azumin zakisha mamaki.

“Da haka mahaifiyata zata karanta ayar psalms da kumburarren ido da hannu duk jini gashi tana azumi.

“Dukan bai tsagaita ba, a ranarta 19 da daukar azumin, mahaifina ya kamata tana zuba masa man neman kariya a rigarsa, gami da karanta ayar psalms ta 40, a zatonsa tayi kokarin halakashi ne da tsafi, hakan yasa ya rotsa ma ta kwalbar giya a kai.

“Ta yanke jiki ta fadi ba tare da sannin inda kanta yake ba har na tsawon kwanaki biyu. Daga baya ta bude idonta ta ce. Ayar psalms 91, sannan ta rufe idonta har abada. Bayan wasu watanni, mahaifina ya auro wata mata, fastonmu yayin daura auren ya ce wa mahaifina.

“Ka lura da kyau, don ka rasa wani tsohon abu dole rayuwa ta cigaba.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe