27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

‘Yan sandan Saudiyya sun tsare alhazan da suka bai wa hammata iska a Makkah

Labarai'Yan sandan Saudiyya sun tsare alhazan da suka bai wa hammata iska a Makkah

Wani faifan bidiyo ya yaɗu a shafukan sada zumunta inda aka ga mutane biyu suna faɗa sanye da Ihrami a unguwar da ke tsakanin Safa da dutsen Marwa a kasar Saudiyya.

Cikin ikon Allah ba a samu wani rauni ba, kuma an ɗauki matakin shari’a kan mahajjatan da suka yi fadan a Saudiyya.

Saudi Fight
‘Yan sandan Saudiyya sun tsare alhazan da suka bai wa hammata iska a Makkah

Yana da kyau mu lura idan muka shiga cikin Ihrami ba ma iya cire gashin kanmu ba balle mu yi faɗa da wani musulmi ba. Da a ce faɗan yasa an samu rauni, da an bukaci su yanka akuya a Makka a matsayin diyya.

Shin hakan ya dace?


Ya zama wajibi mu mutunta alfarmar ɗakin Allah. Jama’a na zuwa Masallacin Harami daga ko’ina a faɗin duniya domin samun nutsuwa da kwanciyar hankali. Nuna irin wannan hali ba za a iya tabbatar da ko wane irin hali yake ba.

Saudiyya ta cire matakan korona, Alhazawa miliyan 2 za su gudanar da aikin Hajjin bana

Ƙasar Saudiyya ta sanar da cewa Alhazawa miliyan ɗaya ne za su gudanar da aikin Hajji a wannan shekarar. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Ƙasar ta sanar da hakan ne a wata wallafa a shafin Twitter wacce ministirin Hajji da Umrah ta yi, inda ta bayyana cewa yawan mutane ya haɗa da Alhazan ciki da kuma wajen ƙasar.

An dakatar da alhazan ƙasashen waje shiga Saudiyya har na shekaru 2

Idan zaa iya tunawa cewa, an dakatar da Alhazan ƙasashen waje shiga ƙasar na tsawon shekaru 2 saboda barkewar annobar cutar korona a shekarar 2020, inda a shekarar 2021 aka bar Alhazai 60,000 kacal ‘yan ƙasar Saudiyya su ka gudanar da aikin Hajji.

Idan komai na tafiya daidai, ƙasar ta na ƙarbar Alhazai miliyan biyu daga kowane sassa na duniya.

An bayyana yadda Hajjin bana zai kasance

A cikin sanarwar, ta bayyana cewa ƙasar ta na son cigaba da adana nasarar da ta samu wajen daƙile annobar korona, wanda hakan ya sanya zaa baiwa mutane ‘yan ƙasa da shekaru 65, damar gudanar da aikin Hajji bayan sun kawo gwajin da ke nuna basu da cutar sa’o’i 72 kafin tasowar su.

Yawan Alhazan da za su zo daga kowace ƙasa wannan shekarar zai zama bisa tsarin abinda aka ƙayyade wa kowace ƙasa duba da amfani da shawarwarin hukumomin lafiya.

Ministirin Hajji da Umrah ta sanar da cewa aikin Hajjin bana zai gudana cikin waɗannan ƙai’dojin: Hajjin bana na mutane ‘yan ƙasa da shekaru 65 ne, sannan kuma sai sun yi allurar rigakafin korona wacce ministirin lafiya ta ƙasar Saudiyya ta amince da ita.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Facebook Page
Twitter Page
WhatsApp Group
Telegram Channel
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe