34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

An damke matashin da ya yi shigar mata a Saudi Arabia har da niqab yayin da zai je wurin budurwa

LabaraiAn damke matashin da ya yi shigar mata a Saudi Arabia har da niqab yayin da zai je wurin budurwa
43623483644 4342aa9fe6 c
An damke matashin da ya yi shigar mata a Saudi Arabia har da niqab yayin da zai je wurin budurwa

Wani dan kasar Masar mai suna Ahmad mai kimanin 22 ya kamu da soyayyar wata yarinya da ya nemi aurenta sau ba adadi amma bai samu karbuwa a wurin mahaifinta ba. Ahmad Ya kasance yana aiki a kasar Saudiyya.

Ya yanke shawarar ziyar tar budurwar sa

Tsautsayi ya sashi yanke shawarar kaiwa budurwarsa ziyara wacce ke zaune a wani kauye mai suna Sowada Abu Shalabi Al Sharqeya. Watarana ya taki sa’a budurwar ta shi ita kadaice a gida iyayenta basa nan sun fita sai Ahmad ya samu damar zuwa gareta. Wannan shawarar ziyara da Ahmad ya yanke ya aminta da ita.

Ya nemi Aron kayan mata

44339747271 884b2287a1 z

Nan take ya nemi aron Abaya a wani wuri domin ya sami damar isa ga budurwarsa. Sanya abayar sa ke da wuya sai ya tunkari gidan budurwar ta sa. Amma saboda batan basira sai ya manta ya chanza takalmin kafar sa.

A halittar mace da namiji akwai banbanci

Allah ya halicci maza da mata da kira maban banta.Nan take mutanen kauye suka gane cewar Ahmad namiji ne hakan ya faru ne daga yanayin salon tafiyarsa da kuma takalman kafansa. Yana gab da isa gidan budurwar ta sa mutane kewayen suka dakatar da shi tare da cire Abayar jikin sa,nan take jama’ar kauyen suka farmasa da duka inda suka yi masa dukan tsiya saboda suna son tunatar da shi manufar sa akan aikata hakan.

Yanzu dai an kama Ahmad kuma har yanzu ba a gama bincike akan faruwar wannan lamari saboda ko al’umma bata yadda da irin wannan lamari ba balle kuma hukumomi.
To matasa gareku,kunga dai yadda soyayya ta ja wa wani matashi shan na jaki.

Baturiyar da ta halaka saurayinta dan Najeriya a kasarsu ta ci gaba da walwalarta, har da zuwa mashaya

An ga wata baturiya da ta halaka saurayinta dan Najeriya ta hanyar daba masa makami a mashaya tana shan giya tare da mahaifinta, yayin da dangin wanda ta halakan suke zaman makoki, LIB ta ruwaito.

Courtney Tailor Clenney ta halaka Christian Toby Obumseli, dan Najeriya sannan mazaunin Amurka ta hanyar daba masa wuka a ranar Lahadi, 3 ga watan Afirilu, a mazauninsu dake Miami.
Anyi ram da Courtney, amma sai tayi barazanar halaka kanta, hakan yasa ‘yan sanda suka mikata ga asibitin mahaukata karkashin dokar Baker.

A Florida, jami’an tsaro na da damar mika mutum asibitin mahaukata na tsawon kwanaki uku ta hanyar amfani da dokar kasa ta Baker.
An ganta a mashaya tare da mahaifinta a daren Juma’a, 8 ga watan Afirilu, sai dai wata mata ‘yar Najeriya, Nnenna da ta ganta ta fatattaketa daga mashayar.

“Eh, ki tafi. Ki tafi, saboda kin halaka saurayinki,” An jiwo Nnenna na fadawa Courtney.

An take Courtney da mahaifinta suka bar mashayar.

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe