34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Ramadan 2022: Hanyoyi da lokacin gane daren laylatul Qadr cikin sauki

LabaraiAl'adaRamadan 2022: Hanyoyi da lokacin gane daren laylatul Qadr cikin sauki
005ab5c89b62ce4f
Ramadan 2022: Hanyoyi da lokacin gane daren laylatul Qadr cikin sauki

Daren Laylatul Qadr darene da dukkan musulmi suke fatan dacewa saboda falalarsa,fai’dojin sa da kuma albarkar da ke cikin wannan dare.

Ibadar da ake yi a cikin wannan dare daidai ta ke da ibadar shekaru 84— a cewar WhyIslam.org.
Sura ta 97 a cikin Al-Qur’ani mai girma ta yi cikakken bayani ga me da daren inda ayar take cewa: “Mun saukar da shi (Alkur’ani) a cikin daren lailatul kadari. Kuma me zai sanar da kai daren Lailatul Qadri? Daren lailatul qadari yafi watanni dubu. Mala’iku da Ruhi suna sauka a cikinsa, da iznin Ubangijinka, tare da kowane umurni. Amincinta ya tabbata har zuwa ketowar alfijir.” (Q. 97).
Daren lailatul Qadr mafi yawan lokuta yana fadowa a goman karshe na watan Ramadan.

Bidiyon matasan Kiristoci suna raba wa Musulmai abinci a watan Ramadan

Wata kungiyar matasan kiristoci, sun hada kansu domin yin wani aiki da jama’a da dama suka kira a matsayin na jin kai.

Sun raba abinci ne ga musulmai matafiya masu azumi, domin suyi bude baki da shi, a babban birnin Dakar dake kasar Senegal.
Faifan bidiyon da aka gani a yanar gizo, ya nuna matasan suna baiwa matafiyan kunshin abinci domin sanya musu farin ciki.

Musulmai da kiristoci a kasar Senegal, suna zaune da junan su lafiya. Iyalai da zaka samu gambiza ce ta hadakar musulmai da kiristoci.
Mutane da yawa da suka kalli bidiyon da @trtworld ya yada a shafin sa na instagram, sun yi sharhi kamar haka :

@in.the.shadows.of.malec yace :

“Kai abin mamaki”

@generouspappi yace :

“Dama fa mu da kanmu zamu samarwa da kanmu lumana a muhallin mu”.

@nourom.ar yace :

“Mutunta mutum yakamata, sannan kuma tilas ne mu mu kula da kasar mu, koda kuwa wanne irin addini muke yi, a ko ina a duniya ”
@x.a_ray_of_light.x yace :

“Dama haka ya kamata abin ya kasance, mutunta juna da taimakon juna.. Wannan shine abin da musulunci da sauran littattafan gaskiya suka koya mana… Wannan shine mutuntaka”.

@kahfy_ateecck yace :

” yada kauna da abin kirkin.. Yayi kyau “.

@sureyyadalgin yace :

“Amma matasan musulmai kuwa suna yin haka ga sauran Addinai? Idan har suna yi to kuwa na sara musu.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe