24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Mata ku koyi kulawa da jiki: Namijin da ya fara daukar ciki a duniya ya koma cakaras bayan haihuwa ta 3

LabaraiMata ku koyi kulawa da jiki: Namijin da ya fara daukar ciki a duniya ya koma cakaras bayan haihuwa ta 3

Ko kun taba jin labarin mutum na farko a duniya da ya taba daukar juna biyu?

Duk da bai yi kama da maganar da hankali zai dauka ba, amma da gaske ne, Legitnaijanews.com ta ruwaito.

ciki
Mata ku koyi kulawa da jiki: Namijin da ya fara daukar ciki a duniya ya koma cakaras bayan haihuwa ta 3

A cewar wani mutum mai suna Thomas an haifesa a mace, amma tuntuni yasan da cewa ya so zama namiji, saboda haka yana da shekaru 20, ya fara allurar testosterone (sinadin kwayoyin halittar maza), wanda ya yi sanadiyyar bayyanar sajensa, kankantar masa da murya da rage masa mazantaka.

A shekarar 2012, ya yanke shawarar yanke nonuwansa, yayin da matarsa ta cire mahaifarta.

Amma a wannan lokacin, Thomas ya yanke shawarar barin al’aurarsa ta mata.

Duk da ta hanyar dashe aka sanya masa ‘da. Amma a halin yanzu yana warkewa bayan ya haifi ‘ya’ya uku.

Kaduna: Yarinya mai shekaru 12 da malami ya ɗirkawa fyaɗe ta haifi ɗa namiji

Wata yarinya ƴar shekara 12 a duniya wacce wani malamin makaranta yayi wa fyaɗe a unguwan Fantaro cikin ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna, a wajajen watan Yunin 2021, ta haifi ɗa namiji. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Malamin ya yaudare ta sannan yayi mata fyaɗe

Halima (ba sunanta na gaskiya ba) tana sayar da chin-chin, a ƙauyen su, lokacin da malamin mai suna Salihu ya yaudare ta cewa zai sayi chin-chin na N200.

Salihu ya rufe mata baki sannan yayi mata fyaɗe a cikin ɗakin.

Daily Trust ta samo cewa yarinyar ta ɗauki juna biyu watanni uku bayan aukuwar fyaɗen, inda aka miƙa ta a hannun ministirin jinƙai da walwala ta hannun gidauniyar Ummulkhairi Foundation.

An tabbatar da haihuwar yarinyar

Sai dai, yayin da ta ke tabbatar da haihuwar yarinyar, kwamishiniyar jinƙai da walwala ta jihar, Hajiya Hafsat Baba, ta bayyana cewa yarinyar ta haifi ɗa namiji cikin nasara.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe