24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Watan Ramadan: ‘Yan sandan Kano sun haramta yin ‘Tashe’ a jihar

LabaraiWatan Ramadan: ‘Yan sandan Kano sun haramta yin ‘Tashe’ a jihar

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kanota hana yin ‘Tashe’ wata al’ada wacce ake yi duk shekara da watan Ramadan na kwanaki 10 na farko.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana hakan a wata takarda wacce ya saki a ranar Litinin 11 ga watan Afirilu, i da ya ce akwai bata-garin da suke amfani da tashe suna tafka barna, Daily Nigerian ta ruwaito.

tashe
Watan Ramadan: ‘Yan sandan Kano sun haramta yin ‘Tashe’ a jihar

Kamar yadda Kiyawa ya ce:

“Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano tana farin cikin sanar da jama’a cewa ta dakatar wasan gargajiya (Tashe) wanda ake yi a ranakun farko 10 na watan Ramadan.

“Hakan ya biyo baya yadda wasu bata-gari suke amfani da tashen wurin aiwatar da miyagun ayyuka kamar sara-suka, kwacen wayoyi da shaye-shaye.”

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ma ya yi kira ga mazauna jihar, muasamman iyaye da su ja kunnen yaransu daga keta dokoki.

Takardar ta ci gaba da cewa:

“Duk wanda aka kama yana keta dokoki za a ladabtar da shi. Muna yi wa kowa fatan yin azumi lafiya.”

Malaysia ta haramta ci ko sha a cikin jama’a a watan Ramadan, za a fara ɗauri ko cin tara

Hukumomin Malaysia sun sanar da cewa za a kama duk Musulmin da aka gani yana ci ko sha a bainar jama’a batare da wani lalura ba yayin azumin watan Ramadan, za a yanke musu hukuncin tara ko dauri, ko kuma duka biyun.

Za a ci tarar duk wanda aka kama yana ci ko sha a cikin jam’a

Mataimakin babban ministan Penang I Datuk Ahmad Zakiyuddin shi ne ya bayyana cewa za a gurfanar da wadanda suka karya wannan doka a karkashin sashe na 15 na dokar hukunta laifuka ta Penang ta shekarar 1996.
Ya kara da cewa a cikin watan Ramadan jihar Penang da ke kasar Malaysia za ta gudanar da wani shirin hadin gwiwa, wanda hakan na daya daga cikin kokarin da mahukuntan kasar suke yi don ganin an wayar da kan al’ummar musulmi da kuma gayyatarsu domin martaba wannan wata na ramadana.

Hukumar ta ce wannan yunkuri zai kawar da duk wani aikin mara kayau a watan na ramadana

Wannan aiki na hadin gwiwa zai kawar da ayyukan da suka sabawa watan Ramadan, kamar cin abinci da sha da gangan a bainar jama’ar batare da wani laluri rashin lafiya ba.

Duk wanda ya aikata wannan laifi a karon farko, to za a ci tarar sa RM1,000 ko kuma zaman kurkukun wata shida ko kuma duka biyun.

Idan aka sake maimatawa a karo na biyu za a ci tarar RM2,000 ko ɗaurin shekara ɗaya ko duka biyun.
A cewar Ahmad Zakiyuddin, wanda shi ne shugaban kungiyar Penang Islamic Religious Council (MAINPP), doka ta 15 ba wai masu abincin kawai ta shafa ba, har ma da masu sayar da abinci, da abubuwan sha, irin su sigari, da dai sauransu.
Ya ce, Sashen Harkokin Addinin Musulunci na Penang (JHEAIPP), Majalisar Penang City (MBPP), Majalisar City na Seberang Perai (MBSP), Ma’aikatar Lafiya ta Penang, da Sashen Gudanar da Ayyukan Halal na JHEAIPP za su yi aiki tare don gudanar don hadin gwiwa wajen ganin an kawar da masu karya doka.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe