24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Yadda dattijo ya yi ‘yaji’ ya kwashe kayansa bayan ya gano matarsa da suka yi shekaru 30 tana soyayya da wani

LabaraiYadda dattijo ya yi 'yaji' ya kwashe kayansa bayan ya gano matarsa da suka yi shekaru 30 tana soyayya da wani

Wani mutum ya kwashe kayansa bayan gano yadda matarsa ta ha’inceshi duk da tsawon shekarun da suka yi a tare, Legit.ng ta ruwaito.

Mijin ya kama matar tasa da suke da yara 4 tare tana shanawa da wani saurayinta tun na makarantar sakandare.

Ya ce yanzu haka ya koma wani gida mai daki daya daga nan yake wucewa wurin aiki yayin ca yaransa suke kai masa ziyara kullum.

mai yaji
Yadda dattijo ya yi ‘yaji’ ya kwashe kayansa bayan ya gano matarsa da suka yi shekaru 30 tana soyayya da wani

Mutumin wanda ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar Twitter ne ya shaida yadda ya yi asarar shekaru 30 na rayuwarsa tare da matarsa wacce bata cancanci hakan ba.

Kamar yadda ya yi wallafar a rana Asabar, 9 ga watan Afirilu, ya ce matarsa ta kama soyayya da saurayinta na sakandare tun shekaru 2 da suka gabata.

Ganin wannan lamarin ne ya sa ya bar gidan ya samu wani daki ta ci gaba da rayuwa.

Bayan rabuwarsu ta sake aure

Kamar yadda ya wallafa:

“Na fuskanci wani kalubale, yanzu haka ina cikin damuwa bayan shekaru 30 da aure har da yara 4 na gano yadda matar da nake matukar so take kula wani daban.

“Yanzu haka na yi yaji na bar mata gidan sannan na koma na kama hayar wani gidan inda yarana suke zuwa suna gani na a ofishina ina ba su kudin harkokin yau da kullum.

“Yau shekaru 2 kenan da na bar mata gidan bayan na kamata da wani wanda ta ke fada min cewa dan ajinsu ne na sakandare. Kenan na yi asarar shekaru 30 din rayuwata.”

Magidanci Cosmas da ya ci N755m a caca ya sayi katafaren gida, ya gwangwaje matarsa da kyautar tamfatsetsen otal

An kira Cosmas Korir a waya ne, inda aka shaida masa cewa yaci (Ksh) wato kudin kasar Kenya miliyan dari biyu da takwas 208m , wanda yayi daidai da Nairar Nageriya miliyan dari bakwai da hamsin da dubu dari biyar da casain da daya, da dari bakwai da goma N755, 591, 710


Ya karkata kudaden zuwa halattaccen kasuwanci, inda ya dinga siyawa kansa gidaje, da filaye. 

Tsohon dan takarar majalisa daga yankin Pokot ta yamma, a kasar Kenya, Cosmas Korir, ya tuna wani kiran waya cikin marari, wanda ya canja rayuwar sa har abada. 


Kiran waya ne wanda mutane kadan ne suke samun irin sa a rayuwar su, kiran da aka shaida masa cewa shine wanda ya lashe zunzurutun kudi har kimanin Ksh 208,733,619 wanda a kimar kudin Najeriya ya kama, Naira 755,591, 710
Da yake magana a gidan talabijin na Gamblers Paradise, Cosmas din yace, koda yaushe gidan yana cin nasara, kuma ya bayyana cewa yana tuki ne yayin da kyakkyawan labarin ya sameshi. 

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe