27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Jerin matan Kannywood 6 da aurensu ya mutu suka dawo harkar fim dumu-dumu

LabaraiKannywoodJerin matan Kannywood 6 da aurensu ya mutu suka dawo harkar fim dumu-dumu

A shekarar nan an samu mace-macen aure daban-daban a shekarar 2022 musamman a masana’antar Kannywood.

Sai dai sukan ce a ko yaushe kuma a ko ina aure yana mutuwa amma tasu ta fi fitowa kasancewar sanannu ne.

  1. Zarah Diamond
zara diamond
Zara Diamond

Fitacciyar jarumar ta yi aure ne a shekarar 2021 wandaya kasance na sirri don bata sanar da mutane da dama ba, Arewa Package TV ta ruwaito.

Sai dai daga baya aka samu labarin mutuwar auren nata wanda daga baya ta dawo ta ci gaba da harkokinta da wallafe-wallafenta a kafafen sada zumunta.

  1. Rahama Hassan
rahaaama hassan
Rahama Hassan

Jaruma Rahama ta yi aure a shekarar 2017 ne, sai dai ta bayyana a wani bidiyo wanda Furodusa Abubakar Bashir Mai Shadda ya wallafa na ‘yan kungiyar 13 times 13 suka yi.

Wannan bidiyon ne ya tabbatar da cewa aurenta ya mutu saboda sun yi hoton gab da gab kuma shigarta bata yi kama da ta matan aure ba.

  1. Mansura Isah
Mansura Isah

Jaruma Mansura Isa tsohuwar mata ce ga jarumi Sani Danja wadanda auren nasu yake cikin aure mafi karko a cikin na ‘yan Kannywood.

Sai dai auren nasu ya samu matsala ne a shekarar 2021 inda har ta kai su ga rabuwa. Jarumar ta dawo Kannywood dagaske har ta ci gaba da harkokinta da sana’arta.

  1. Maryam Malika
Maryam Muhammad Malika

Maryam ma jaruma ce wacce ta yi tashe a masana’antar, kuma ta yi aure ne a shekarun da suka gabata.

Sai dai bayan mutuwar auren ta dawo Kannywood inda ta ci gaba da fina-finai kamar yadda ta yi a baya.

  1. Amina Uba Hassan
Amina Uba Hassan

An fi sanin jarumar da Amina Rani ko kuma maman Haidar. Tsohuwar jarumar Kannywood din mata ce ga Adam A. Zango a baya kuma ita ce mahaifiyar babban dansa, Haidar.

Bayan mutuwar aurensu ne ta dawo fim wanda a baya ta yi tun kafin aurensu na farko. Yanzu haka ta bayyana a fina-finai kamar Gidan Danja, kuma ta dawo masana’antar da karfinta.

  1. Fati Muhammad
Fati Mohammed

Jaruma Fati Muhammad tana cikin jaruman da aka yi yayi a masana’antar, kuma ta ja zarenta sosai don ta samu shuhura mai yawa.

Ta yi aure sau biyu wadanda duk basu yi karko ba. Amma yanzu haka ta dawo masana’antar inda ta ke ci gaba da harkokinta.

Jerin jaruman Kannywood mata 4 masu hawa motoci masu tsadar gaske

A lokuta da dama mutane na yawan sanya alamar tambaya kan yadda wasu daga cikin jaruman mata ke tafiyar da rayuwar su, musamman ma yadda suke kashe makudan kudade wajen sayen kayan kyale-kyale na rayuwa.

Hakan ya sanya wasu ke yawan tambayar a ina suke samun irin wadannan kudade da suke irin wannan rayuwa da su, tabbas kowa ya san da yawa daga cikin jaruman banda sana’ar da suka saba ta Kannywood suna hadawa da kasuwanci da kuma ‘yan sauran abubuwan da ba a rasa ba.

A wannan karon Labarun Hausa ta binciko muku jerin manyan jaruman Kannywood mata da suke hawa dankara-dankaran motoci na kece raini:

1. Jaruma Hafsat Idris

Ta siya motar kirar Formatic, mai tsadar kimanin Naira miliyan goma sha bakwai (N17,000,000).
A lokacin da ta siya ta girgiza masana’antar Kannywood kwarai. Ta kuma wallafa hotunan motar a shafinta na Instagram inda ‘yan uwa da abokai su ka dinga yi mata fatan alkhairi.

Abokan sana’arta ma sun dinga wallafawa a shafukansu su na mata fatan alkhairi ciki har da sarki Ali Nuhu wanda ake yi wa kallon aboki kuma amininta a masana’antar

2. Jaruma Hadiza Gabon

A lokacin jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram inda ta nuna godiyarta kwarai ga kawar. Farashin motar ya kai naira miliyan goma sha daya(N11,000,000).

3. Motar Jamila Nagudu

Shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya ba jarumar kyautar mota kirar Toyota Matrix.

A shafin Rarara Multimedia na instagram mawakin ya wallafa bidiyo inda aka ga ya na ba jarumar kyautar motar inda ta nuna farincikinta kwarai.

Dama mawakin ya saba yi wa abokan sana’arsa na fim kyautuka iri-iri, lallai jarumar tayi matukar jin dadin kyautar.

4. Fati Washa

Ta yi sabuwar motar kirar toyota wacce abokin aikinta su ka wallafa su na taya ta murna.
Jarumar tana daya daga cikin taurarin da su ke hasakawa a masana’antar bayan ta taka rawa a fina-finai da dama.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe