27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Matashi ya hau bene hawa 15 domin ceto mahaifiyarsa da gobara ta ritsa da ita

LabaraiMatashi ya hau bene hawa 15 domin ceto mahaifiyarsa da gobara ta ritsa da ita


Wani matashi da shekara 35, mai suna Jermaine, ya sha alwashin sai yayi nasarar tseratar da mahainciyar sa, ba tare da la’akari da cewa zai dauki kasadar hawa bene mai matukar tsayi ba. 


An gano shi a cikin bidiyon yana ta kokarin daukar dala ba gammo, domin ceto mahaifiyarsa wadda wuta ta tsare, a hawa na 15 na kololuwar bene. 


Rukunin benayen Westpark dake titin Holden, a garin Philadelphia dake Amrika, ya fara cin wuta   a ranar Alhamis, nan take sai Jermaine ya sami kira daga wani dan uwan sa, inda ya shaida masa cewa babar sa Shella ta kasa fita, inda yayi hanzari ya isa wurin. 

Yadda matashin ya shiga gurin gobarar


Da farko Jermaine din yayi kokarin shiga ta hanyar gaba, amma jami’ai basu bashi dama ba, saboda 

” sun ce madaga bata aiki, ni kuma nace, ba matsala, zan yi haye. Kawai dai ina so in tabbatarda cewa baba ta – baba ta tayi rauni, ta kwanta kasa. Saboda haka ina da bukatar lallai na isa inda take”

Jermaine din ya bayyana wa kafar ABC 7.


“Sai suka ce, baza mu baka hanya ba, Nine fa nace naji na gani saboda baba ta ce, bai kamata a tsareni ba, wannan fa baba ta ce”. 


A matsayinJermaine wanda ya nakalci tako-tako saboda aikin rufi da yake yi, kuma mutum mai cike da kwarin gwiwa, bai kariya ba, kawai sai ya yanke shawara ya hau kan ganin ta hayar amfani da filaya yanke waya. 


Kafin wannan ranar, Jermaine din ya ji rauni a kugun sa, sakamakon faduwa da yayi a matakalar bene, amma wannan ciwo bai hana shi hawa ganin ba. 


“Lokacin da na sami  kofa a can mashiga ta saman ginin akwai wani dandamali, kuma sai na taka wannan dandalin, Inda na isa zuwa daya kofar, sai kuma naci gaba da hawa kai tsaye”

Jermaine din wanda dama ya san ciki da bai na gidan, tun lokacin da shima ya zauna a gidan a can baya, ya bayyana. 

Sun yi magana da babarsa ya tabbatar tana raye


Yayin da ya isa inda babarsa ta makale a hawa na biyar, sai ta shaida masa cewa tana lafiya, amma har yanzu wuta tana ci. Bata hana shi hawa ginin ba, koma yana tafiya daidai,

“Kawai rudewa tayi, amma batayi mamakin abin da nayi domin  ceton ta ba, saboda ta san zan iya yin abin da yafi haka ma domin ta” 

Daga nan sai Jermaine din ya sakko kasa, inda ya nemi jami’an da su kama shi, akan abin da yayi. Daga baya, sai jami’an suka yanke cewa an bar shi ya tafi,

” Da can kuma, a gurin a baya yace mini, kai tsaye daga gurin za’a ingiza keya ta zuwa gidan yari, sabida wai ai aikin sa ne, nake yi. Koma dai menene ya daga mini kafa, ya gane girman lamarin, ya gane cewa, idan hankali ya tashi kuma babbar mutum tana ciki, tabbas tana halin kaka nakayi saboda haka dole ne kayi duk abin da zaka iya”

Jermaine din ya fada.


Haka kuma, mahaifiyar Jermaine din da wasu mazauna gidan sun fita salun-alun, wasu guda 4 kuma da jami’an kashe gobara 3 an garzaya dasu asibiti saboda shakewar hayaki.

Babu gobarar da ta tashi a ma’aikatar kuɗi ta tarayya a Abuja

 Wasu rahotanni daga jaridu sun bayyana cewa, an samu ɓarkewar gobara a hedikwatar ma’aikatar kudi ta tarayya da ke Abuja da safiyar Laraba.

Babu cikakken labarin abubuwan da suka faru a lokacin da wannan rahoto ya fito amma shafukan sada zumunta sun nuna hayaki ya turnuƙe ginin da ke tsakiyar cibiyar kasuwanci ta babban birnin tarayyar ƙasar.

Jami’an kashe gobara kuma suna ta fafata don shawo kan gobarar.

A cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na twitter, ma’aikatar ta danganta lamarin da wani baturi da ke ajiye waje guda, inda ta ce an shawo kan lamarin.

“Wuta ba ta ci hedkwatar ma’aikatar kudi ta tarayya kamar yadda aka ruwaito a shafukan sada zumunta ba. Maimakon haka, an samu wani abin da ya faru a kan hanya a cikin ginshiƙi wanda ya haɗa da keɓaɓɓen ƙunshi baturi (inset na hoto). Jami’an tsaro da ke bakin aiki ne suka fitar da shi cikin gaggawa,”__ in ji wallafar ta Twitter.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe