34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Jikina har rawa yake idan na tuna irin ayyukan alkhairin da zan yiwa ‘yan Najeriya idan na zama shugaban kasa – Amaechi

LabaraiJikina har rawa yake idan na tuna irin ayyukan alkhairin da zan yiwa 'yan Najeriya idan na zama shugaban kasa - Amaechi
5d2a38421cebc8b6
Jikina har rawa yake idan na tuna irin ayyukan alkhairin da zan yiwa ‘yan Najeriya idan na zama shugaban kasa – Amaechi

A karshe dai Rotimi Amaechi, ministan sufuri, ya bayyana kudurinsa na son tsayawa takarar shugaban kasa a ya bayyana hakn,ne a ranar Asabar, 9 ga watan Afrilu, inda ya bayyana yadda zai magance matsalar rashin tsaro da yunwa da ake fama da shi a kasa Najeriya. Amaechi ya bayyana wannan kudiri nasa ne yayin wani taron godiya na musamman da jam’iyyar All Progressives Congress ta shirya a filin wasa na Adokiye Amiesimaka da ke Igwurita a karamar hukumar Ikwerre, wani wurin gangami da ya gina a lokacin yana Gwamnan Jihar Ribas.

Zan tsaya takara badan ra’ayin kaina ba sai don kawai in fito in gwada tawa basirar wajen ciyar da kasa gaba
Ministan wanda a cikin jawabinsa ya bayyana cewa burinsa na son tsayawa takara ba wai dan ra’ayin kansa ne,sai dan ya kasance dolensa ya fito domin bayyana irin nasa kokarin inji rahoton The Punch.
Ministan a cikin jawabinsa mai taken ‘ Ci Gaba ta re da jajircewa’ inda ya fara da rera waka “waye zai ja da hukunci Ubangiji’, yana mai cewa ‘Akwai nasarar na nan tafe’,
ya ce: ya ku ‘yan uwana ‘yan Najeriya yau gani tsaye a gabanku domin in bayyanar muku da kudirina na son tsayawa takarar shugabanci kasa Najeriya, “Burina na son tsayawa takara ba wai dan ra’ayin kaina ba ne sai dan saboda sauke wani hakkin da ya rataya a kaina domin hidimtawa kasa.”
jikina har rawa yake domin ganin na kawo sauyi mai mahimmanci a rayuwar dukkan ‘yan Najeriya.”
Amaechi, wanda ya nemi ayi addu’a ga wadanda suka rasa ransu a harin jirgin kasa da ya rutsa da su daga Abuja zuwa Kaduna, ya yi Allah wadai ga rashin tsaro, da kuma rashin aikin yi da yunwa da suka addabi kasar.
Ya kara da cewa: “Na yi alkawari da zuciyata da jikina da ruhina wajen ciyar da Najeriya gaba domin ganin kowani dan Najeriya ya samu ilimi, kowane matashi zai samu aiki ko tallafi don fara kasuwanci, kowane dan kasa zai yi walwala cikin aminci.

Waɗanda su ka gagara ceto kan su wai su ne za su ceto Najeriya, Ministan Buhari ya ragargaji PDP

Ƙaramin ministan ƙwadago, Mr Festus Keyamo, ya yi shaguɓe ga babbar jam’iyyar adawa ta ƙasa wato PDP. Ministan yayi wannan shaguɓen ne a wata wallafa da yayi a safiyar ranar Lahadi, 10 ga watan Afrilun 2022.

Ministan Buhari ya soki PDP
Ministan ya ragargaji jam’iyyar akan iƙirarin da ta ke yi cewa za ta ceto ƙasar nan daga halin da ta ke ciki na samun rabuwar kawuna a tsakanin ƙabilun ƙasar.

Jam’iyyar PDP ta daɗe ta na nunawa jam’iyyar APC yatsa kan cewa ta kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin ƙabilun ƙasar nan.

Da ya ke mayar da martani kan zargin da jami’iyyar ta PDP ta daɗe ta na yi, Mr Festus Keyamo ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta da hurumin yin wannan zargin ga APC tun ta ƙasa haɗa kawunan ƙabilun da ke cikin ta.
Mr Festus Keyamo ya ce:

Waɗanda ke sukar mu cewa mun raba kawunan ƙabilun Najeriya, sun kasa haɗa kawunan ƙabilun jam’iyyar su; a wajen neman takarar shugaban ƙasa, sun yi nasarar raba kawunan ƙabilun jami’iyyar su. Waɗanda su ka kasa ceto kan su, suna son su ceto Najeriya

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe