36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Jihohi 8 da PDP za ta iya rasawa lokacin zabe idan ta tsayar da dan Arewa takarar shugaban kasa

LabaraiJihohi 8 da PDP za ta iya rasawa lokacin zabe idan ta tsayar da dan Arewa takarar shugaban kasa
da4f81fdd29a2789
Jihohi 8 da jam’iyyar PDP zata iya rasawa lokacin zabe idan ta fitar da dan Arewa takarar shugaban kasa

An ji jita-jitar cewa jam’iyyar PDP zata iya shan kaye a wasu jihohi idan har su ka kuskura su ka fitar da dan takara daga yankin Arewa,Sai dai Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe wanda shine shugaban kwamitin shiyya na jam’iyyar PDP ya karyata wannan lamarin da ya bayyana.

Kwamitin shiyayya ta bayyana wannan kuduri a bayyane amma ba a hukumance ba

Ya ce kwamitin shiyya ta yi yunkuri akan wannan kuduri amma har yanzu kwamitin zartarwa na kasa (NEC) bata aminta da shi ba. Jaridar Thisday ta yi nata hasashen kan abin da ka iya faruwa ga jam’iyyar PDP a zaben 2023 idan har jami’iyyar ta fitar da tikitin tsayawa takara shugaban kasa har dan Arewa yayi nasarar wawurewa a zaben fidda gwani.

Jam’iyyar PDP za ta iya rasa madafun iko in har dan takara ya fito daga yankin Arewa

A cewar jaridar, jam’iyyar ta PDP na iya rasa wasu daga cikin manya manyan jihohin kudancin kasar idan har ta fitar da dan takara daga yankin Arewa. Hakan ya sabawa madogarar fidda dan takarar da zai gaji shugaba Buhari a shekarar 2023.
Rahoton ya fitar da jaddawalin jerin jihohin da jam’iyyar ta PDP za ta iya shan kaye a zaben gwamnoni na shekarar 2023 idan ta yi kunnen uwar shegu ta fitar da dan takara daga yankin Arewa.
Ga jerin jihohin:
Oyo
Delta
Rivers
Abia
Enugu
Akwa Ibom
Benue
Ko da dai jihar ta cross River mamaye take da ‘yan jam’iyyar APC amma anyi hasashen cewa jiha ce da jam’iyyar PDP ta ke da karfi sosai.

Ina tausayin Baba Buhari, ya rasa masu taimaka masa akan rashin tsaro, Gwamna Bala Mohammed

Gwanma Bala Muhammad ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasa masu mara masa baya wajen shawo kan matsalar rashin tsaro, LIB ta ruwaito.

Yayin jawabi lokacin da yake raba ababen hawa ga hakimai da shugabannin kananun hukumomi a jihar Bauchi, Bala ya ce akwai bukatar hada kai da gwamnatin tarayya don yi wa lamarin tsaro garal bawul.
Ya kara da bayyana yadda ‘yan bindiga suka kai wa daya daga cikin kananun hukumomi a jihar Bauchi farmaki cikin kwanakin nan.

A cewar Bala;

“Ba abun amincewa bane gwamnatin tarayya ta cigaba da cewa ba za ta iya tsare kasar nan da yankunan mu ba.

“Muna da kayan aikin da zamu iya haka. Gaskiya ina tausayin Babanmu, Shugaban kasa sannan kwamandan rundunar sojin Najeriya. Saboda yanaso ya yi amma bai samu masu mara masa baya ba.
Ni a matsayin gwamna, shugaban wani bangaren kasar, a shirye nake da inyi aiki tare da gwamnatin tarayya don tabbatar da mun tsare kasarmu da jiharmu. Wannan aikinmu ne baki daya.”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe