34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

‘Yan bindiga sun farmaki ƙauyuka da dama a jihar Filato, sun ƙona gidaje masu yawa

Labarai'Yan bindiga sun farmaki ƙauyuka da dama a jihar Filato, sun ƙona gidaje masu yawa

‘Yan bindiga sun kai farmaki a wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Kanam ta jihar Filato ranar Lahadi, inda su ka ɗauke wasu daga cikin mazaunan garin sannan su ka ƙona gidaje da dama. Jaridar Daily Trust ta rahoto

‘Yan bindigan sun halaka mutane da yawa

A cewar wasu daga cikin mazaunan ƙauyukan, ‘yan bindigan sun kai harin ne a ƙauyukan Kukawa, Gyanbahu, Dungur da Keram, inda su ka halaka mutane da dama.

An bayyana yadda lamarin ya auku

Wani mazaunin ƙauyen Kukawa, Adam Musa, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa an raunata mutane da dama, yayin da mutane da yawa su ka arce daga gidajen su, inda ya ƙara da cewa jami’an tsaro ba su ƙaraso ba har ya zuwa yanzu.

Musa ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun farmaki ƙauyukan da misalin ƙarfe 11 na safe lokacin da mutane ke gudanar da harkokin rayuwar su.

Ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun ƙona gidaje da dama a ƙauyukan.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, yayi alƙawarin sake tuntubar wakilin Daily Trust dangane da lamarin nan ba da jimawa ba.

Yan bindiga sun halaka DPO, ‘yan sanda biyu da ‘yan sakai huɗu a jihar Neja

‘Yan bindiga a ranar Talata sun kai hari ƙauyen Nasko cikin ƙaramar hukumar Magama ta jihar Neja, inda su ka halaka Divisional Police Officer (DPO), Chief Superintendent of Police (CSP) Umar Mohammed Dakingari, ‘yan sanda biyu da wasu ‘yan sakai mutum huɗu. Jaridar Independent.ng ta rahoto

‘Yan bindigan sun dawo ɗaukar fansa

Wata majiya ta bayyana cewa ‘yan bindigan sun dawo ɗaukar fansa ne bayan an kai musu farmaki a wajen ɓuyar su sannan aka ƙwato shanaye a hannun su.

Ba a daɗe ba, DPO ya jagoranci tawagar ‘yan sanda da kuma ‘yan sakai a wani aiki wanda yayi sanadiyyar halaka ‘yan bindiga da dama da kuma ƙwato shanaye sama da 800.

Yana cikin ganawa da jami’an sa domin kitsa wani sabon aikin lokacin da ‘yan bindiga su ka mamaye ofishin ‘yan sandan sannan su ka fara harbi kan mai uwa da wabi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe