Fitaccen jarumin masana’antar Kannywood, Tahir Fagge wanda ya fi bayyana a matsayin uba a fina-finai yana shan caccaka bayan wani bidiyonsa yana tikar rawa tare da wata budurwa ya bazu a kafafen sada zumunta.
Bidiyon nasa ya janyo mutane suna ta maganganu marasa kyau akan masa’antar har wasu suna ganin bai dace dattijo irinshi ya yi irin wannan rawar ba, Masarauta Entertainment ta Youtube ta ruwaito.

Bidiyon ya ja wasu suna ganin babu wani abin fadakarwa a masana’antar Kannywood in baya ga lalata tarbiyyar jama’a.
A bidiyon ko da gani a gidan gala ne dattijon ya kwashi rawa tare da wata budurwa wacce a shekaru ya haife ta inda rawa ya kai shi har da faduwa kasa.
An ga inda ya hau kan wata waka yana wani rawa wanda matashi ne ya dace ya yi wanda har mutane suka nuna rashin jin dadinsu.
Akwai wadanda ke ganin ya kamata dattijo mai shekaru irin Tahir Fagge ya kama kansa don yanzu haka gangara ta kai.
Allah yasa mu dace kuma mu yi tsufa mai kyau. Ameen ya Rabbi.
Ga bidiyon a kasa:
Yadda wata budurwa mara hannaye mai shekaru 27 take rayuwarta cike da walwala
An haifi wata budurwa, Nadia mai shekaru 27 da wata cuta mai suna “phocomelia syndrome”, wacce ta ke janyo nakasu a wurin halittar gabobi.
Kamar yadda shafin Beauty Studio na Facebook ya nuna, ta bayyana:
“Akwai matukar wahala rayuwa a cikin wannan yanayin musamman ga mai karancin shekaru.
“Mutane su dinga kallo na, yara suna tsoro na, idan kuma na wallafa hotunana a kafafen sada zumunta mutane su dinga sukar halitta ta.
Ta ci gaba da cewa yayin da ta ke girma tana fatan samun wanda zai kwantar mata da hankali kuma ya bata kwarin guiwa.
Ta ce tana jin kunyar bayyanar da kanta a gaban mutane. Sai dai daga baya na fahimci cewa babu yadda na iya. Haka nan zan amince da yadda Ubangiji ya yi ni.
Babu wani abin jin kunya a halitta ta saboda haka nan nake. Dakyar na samu na kwantar da hankalina, a cewarta.
Ta ci gaba da bayyana yadda ‘yan uwanta suka dinga kwantar mata da hankali. Yanzu haka tana iya rayuwa kamar yadda kowa ya ke yi.
Mahaifiyarta ta kasance mai ba ta kulawa da kuma kara mata kwarin guiwa, yanzu ta kwantar da hankalinta kuma tana walwala yadda take so.
Ta ce yanzu haka tana farin ciki tare da murna da irin soyayyar da ake ba ta, da abokai da kawayen da ta yi tare da kulawar da ake nuna mata.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com