27.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Waɗanda su ka gagara ceto kan su wai su ne za su ceto Najeriya, Ministan Buhari ya ragargaji PDP

LabaraiWaɗanda su ka gagara ceto kan su wai su ne za su ceto Najeriya, Ministan Buhari ya ragargaji PDP

Ƙaramin ministan ƙwadago, Mr Festus Keyamo, ya yi shaguɓe ga babbar jam’iyyar adawa ta ƙasa wato PDP. Ministan yayi wannan shaguɓen ne a wata wallafa da yayi a safiyar ranar Lahadi, 10 ga watan Afrilun 2022.

Ministan Buhari ya soki PDP

Ministan ya ragargaji jam’iyyar akan iƙirarin da ta ke yi cewa za ta ceto ƙasar nan daga halin da ta ke ciki na samun rabuwar kawuna a tsakanin ƙabilun ƙasar.

Jam’iyyar PDP ta daɗe ta na nunawa jam’iyyar APC yatsa kan cewa ta kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin ƙabilun ƙasar nan.

Da ya ke mayar da martani kan zargin da jami’iyyar ta PDP ta daɗe ta na yi, Mr Festus Keyamo ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta da hurumin yin wannan zargin ga APC tun ta ƙasa haɗa kawunan ƙabilun da ke cikin ta.

PDP
Waɗanda su ka gagara ceto kan su wai su ne za su ceto Najeriya, ministan Buhari ya ragargaji PDP

Mr Festus Keyamo ya ce:

Waɗanda ke sukar mu cewa mun raba kawunan ƙabilun Najeriya, sun kasa haɗa kawunan ƙabilun jam’iyyar su; a wajen neman takarar shugaban ƙasa, sun yi nasarar raba kawunan ƙabilun jami’iyyar su. Waɗanda su ka kasa ceto kan su, suna son su ceto Najeriya

Akwai rabuwar kawuna a PDP

Babban ƙalubalen da jam’iyyar PDP ke fuskanta shine yadda za tayi wajen tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa na shekarar 2023. Jam’iyyar ta na son ta yi watsi da tsarin ƙarba-ƙarba inda zaa baiwa kowane ɗan takara damar neman kujerar ba tare da yin la’akari daga yankin da ya fito ba daga ƙasar nan.

Sai dai, hakan bai yiwa ‘ya’yan jam’iyyar na yankin kudancin Najeriya daɗi ba, waɗanda su ke ganin cewa jam’iyyar yakamata ta fito da ɗan takarar ta daga yankin kudancin Najeriya.

Ana kulla kullalliyar hana Atiku, Saraki da Tambuwal fitowa takara a jam’iyyar PDP

Sarkakiya ta balle a jam’iyyar PDP yayin taron jiga-jiga wanda aka yi a daren Litinin, hakan ya sa shugaban jam’iyyar na kasa, Dr Iyorcha Ayu ya yi gaggawar dakatar da taron zuwa yau, The Nation ta ruwaito.

Hayaniyar ta samo asali ne bayan wasu shugabanni daga kudu suka fara batun cewa a cire mambobin da suka koma APC a baya sannan suka kara dawowa PDP daga cikin jerin wadanda zasu tsaya takarar shugaban kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe