36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Jarumin maza: Hotunan mutumin da ya yi dambe da zaki ya halaka shi bayan ya shiga gidansa

LabaraiJarumin maza: Hotunan mutumin da ya yi dambe da zaki ya halaka shi bayan ya shiga gidansa

Abin mamaki ba ya karewa a duniya, sannan jarumai suna ci gaba da bayyana kansu daga bangarori daban-daban na duniya.

Bayan zaki ya afka wa wani mutum har gidansa, sun kwashi dambe inda mutumin wanda mazaunin Iganga ne a kasar Uganda ya samu nasara akan zakin kamar yadda shafin Wazobia Gist na Facebook ya ruwaito..

jarumin maza
Jarumin maza: Hotunan mutumin da ya yi dambe da zaki ya halaka shi bayan ya shiga gidansa

Yayin tabbatar da aukuwar lamarin, dagacin yankin ya kada baki ya ce:

“Muna jiran a dawo da shi daga asibiti ne din mu ba shi sarauta. Za mu nada shi “Sabon Sarkin Dawa” saboda zakin ya dade yana addabar mutanen kauyen nan.”

Wata tsohuwa wacce ta ga yada lamarin ya auku ta bayyana cewa:

“Sai da cire wa cire wa zakin kai. Wannan mutum ya fusace ya ke, alamu na nuna cewa ya gaji da Uganda da duk wata halittar da ke cikin kasar.”

Sai dai hukumar jami’an kulawa da dabbobin daji ta kasar ta ce sai mutumin ya yi bayani akan dalilinsa na kin tserewa daga zakin kamar yadda doka ta tanadar.

Yanzu haka dai ana jiran ganin dawowarsa daga asibiti don sun yi kare jini biri jini da zakin.

Jarumin maza: Yadda wani mutum ya yi takarar aure da dan Sarkin Aljanu a Kano

Ana zargin wani saurayin matashin aljani da yunkurin kwace wa wani mutum matarsa ta aure, sai dai Allah ya yi wa mutumin taimako, kasancewar sa mai yawan addu’o’i da kuma azkar.

Mutumin ya dage wurin yawaita karatun Al’Qur’ani da addu’o’i a gida da waje har ya samu dakyar matashin aljanin ya kyale masa matar sa.

Bayan nan ne matashin aljanin ya sauya salo, inda ya fara yi wa mutumin tayin kudade masu tarin yawa kimanin Naira miliyan dari uku don ya taimaka ya bar masa matar.

Sun ci gaba da dauki ba dadi da aljanin kamar yadda mutumin ya shaida wa Dala FM:

“Ya ce min shi yana son ta ne tuntuni, in zo mu yi sulhu da shi. Kuma abinda ya sa na aureta saboda ina da yawan addu’o’i da azkar. Kuma shi yana sonta:

“Ya ce min shi dan sarkin aljanu ne. Yake ce min me zai ba ni in bar masa matata? Sai ya ce zai bani miliyan 100 in ina bukata, na ce a’a.

“Sai yace mu yi maslaha ni da shi, kar in zo wurin mai gida Kacaku. Sai yace zai ban miliyan 200 in na yarda. Sai nace mishi gaskiya ni ba irin wannan hanyar nake so ba. Ina dan almajirci na. Ina neman ‘yan hakkoki na wurin Allah.

“Sai yace min in na yarda zai bani miliyan 300, idan ina kokwanto ma yanzu in bude daki na, zan ga kudin. Sai nace mishi a’a.”

Ya ci gaba da shaida cewa shi lebura ne a kasuwa yake yin ‘yan ayyukan sa, don haka ba ya bukatar kudin hannun aljanin.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe