27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Na kasa cin abinci da yin barci tun bayan yankewa mijina hukunci, matar Mulhidin Kano, Mubarak Bala

LabaraiNa kasa cin abinci da yin barci tun bayan yankewa mijina hukunci, matar Mulhidin Kano, Mubarak Bala

Amina, matar Mulhidin Kano, Mubarak Bala, wanda aka yanke wa shekaru 24 a gidan kaso saboda ɓatanci ga Allah da annabi, ta bayyana cewa ta kasa cin abinci sannan barci ya ƙauracewa idanuwan ta tun lokacin da aka tura mijin ta gidan kaso. Jaridar Punch ta rahoto

Mubarak Bala, mai shekaru 37, wanda shine shugaban ƙungiyar ‘yan Adam ta Najeriya, an yanke masa hukunci a Kano bayan kotu ta same shi da amsa dukkanin laifuka 18 da ake tuhumar sa da su, a ranar Talata 6 ga watan Afrilun 2022.

Matar sa ta shiga damuwa sosai

A wata tattaunawa da wakilin jaridar Punch, Amina ta bayyana cewa ta kaɗu matuka tun bayan da aka yanke wa mijin ta hukunci.

Ina ganin mijina duk lokacin da na kulle idona. Bana iya barci. Na kasa cin abinci. Abin ya zama kamar wani mummunan mafarki a gare ni. Ban da wani zaɓi illa na cigaba da haƙuri. Na damu sosai bisa rashin ganin mijina. Ɗa na yana girma ba tare da mahaifin sa a kusa da shi. Wannan abin yayi min yawa sosai.

Mun yi aure a watan Agustan 2019. Ɗa na yana da wata 6 kacal a duniya lokacin da aka tafi da mijina. Ina Abuja lokacin da wani abokin sa ya kirani ya ke shaida min cewa ‘yan sanda sun tafi da shi saboda wata wallafa da yayi akan Annabi Muhammad (SAW) da addinin musulunci. Na kasa fahimtar komai har ya zuwa yanzu da na ke magana da kai.

Za su ɗaukaka ƙara

Amina kuma tayi nuni da cewa za su ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun har zuwa kotun ƙoli.

Dole ne mamallakin Facebook ya san da wannan laifin. Ya san cewa an cafke wani mutum kawai saboda shafin sa sannan an ɗaure shi shekaru 24. Gwamnati ta na sane.

Za mu ɗaukaka ƙara. Ban yarda da wannan hukuncin da aka yiwa mijina ba. Za mu nemo haƙƙin mu har zuwa kotun ƙoli.

Abubuwa 10 da ya dace a sani game da Mubarak Bala, mulhidin da kotu ta ɗaure shekaru 24

Mubarak Bala dan Najeriya ne wanda bai yarda da Allah ba kuma shugaban ƙungiyar ‘yan Adam ta Najeriya. An kama Bala da laifin ɓatanci ga Allah da Annabi…

Mubarak Bala dan Najeriya ne wanda bai yarda da Allah ba kuma shugaban ƙungiyar ‘yan Adam ta Najeriya. An kama Bala ne da laifin ɓatanci ga Allah da Annabi (SWA) don haka aka gurfanar da shi a gaban kotu.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe