24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Saudiyya ta cire matakan korona, Alhazawa miliyan 2 za su gudanar da aikin Hajjin bana

LabaraiSaudiyya ta cire matakan korona, Alhazawa miliyan 2 za su gudanar da aikin Hajjin bana

Ƙasar Saudiyya ta sanar da cewa Alhazawa miliyan ɗaya ne za su gudanar da aikin Hajji a wannan shekarar. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Ƙasar ta sanar da hakan ne a wata wallafa a shafin Twitter wacce ministirin Hajji da Umrah ta yi, inda ta bayyana cewa yawan mutane ya haɗa da Alhazan ciki da kuma wajen ƙasar.

An dakatar da alhazan ƙasashen waje shiga Saudiyya har na shekaru 2

Idan zaa iya tunawa cewa, an dakatar da Alhazan ƙasashen waje shiga ƙasar na tsawon shekaru 2 saboda barkewar annobar cutar korona a shekarar 2020, inda a shekarar 2021 aka bar Alhazai 60,000 kacal ‘yan ƙasar Saudiyya su ka gudanar da aikin Hajji.

Idan komai na tafiya daidai, ƙasar ta na ƙarbar Alhazai miliyan biyu daga kowane sassa na duniya.

Saudiyya
Saudiyya ta cire matakan korona, Alhazawa miliyan 2 za su gudanar da aikin Hajjin bana

An bayyana yadda Hajjin bana zai kasance

A cikin sanarwar, ta bayyana cewa ƙasar ta na son cigaba da adana nasarar da ta samu wajen daƙile annobar korona, wanda hakan ya sanya zaa baiwa mutane ‘yan ƙasa da shekaru 65, damar gudanar da aikin Hajji bayan sun kawo gwajin da ke nuna basu da cutar sa’o’i 72 kafin tasowar su.

Yawan Alhazan da za su zo daga kowace ƙasa wannan shekarar zai zama bisa tsarin abinda aka ƙayyade wa kowace ƙasa duba da amfani da shawarwarin hukumomin lafiya.

Ministirin Hajji da Umrah ta sanar da cewa aikin Hajjin bana zai gudana cikin waɗannan ƙai’dojin: Hajjin bana na mutane ‘yan ƙasa da shekaru 65 ne, sannan kuma sai sun yi allurar rigakafin korona wacce ministirin lafiya ta ƙasar Saudiyya ta amince da ita.

Alhazan da za su shigo daga wajen Saudiyya, ana buƙatar su miƙa gwajin da ke nuna ba sa ɗauke da cutar korona wanda aka yi sa’o’i 72 kafin tasowar su zuwa Saudiyya. Ministirin kuma ta gargaɗi Alhazan cewan dole ne su bi dukkanin hanyoyin kariya domin kula da lafiyar su yayin da su ke gudanar da aikin Hajjin.

Sama da mutum 400,000 za su gudanar da Umrah a watan Ramadan na 2022 a Saudiyya

Bayan shekaru biyu, ƙasar Saudiyya ta cire dukkanin matakan da aka sanya saboda annobar korona akan matafiya ‘yan ƙasashen waje, ciki kuwa har da allurar dole. Haka kuma matakin hana Umrah na tsawon watanni bakwai an cire shi a cikin watan Oktoban da ya gabata.

Alhazai sun yi maraba da cire matakan

Alhazawan da ke da niyyar yin Umrah a cikin watan azumin Ramadan sun ji daɗin sassauta matakan. Hakan ya nuna a yawan mutanen da ake sa ran za suyi Umrah cikin watan azumin bana, kamar yadda mataimakin ministan Hajji da Umrah na Saudiyya, Dr. Abdulfattah Mashat ya bayyana. Ya bayyana cewa masallacin Harami zai amshi baƙuncin alhazai sama da 400,000 cikin watan azumi. Jaridar The Islamic Information ta rahoto.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe