27.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Dadewa akan shadda yayin danna waya na iya haifar da ciwon basir, Likita

LabaraiDadewa akan shadda yayin danna waya na iya haifar da ciwon basir, Likita

Alamu su na nuna akwai dadi sosai idan mutum ya shafe lokaci mai tsawo yana danne-danne a waya yayin da yake kan shadda.

Wani sabon bincike ya nuna cewa akwai yuwuwar mutum ya kamu da ciwon basir idan ya dade yana aikata hakan, Aminiya ta ruwaito.

phone
Dadewa akan shadda yayin danna waya na iya haifar da ciwon basir, Likita

Basir ciwo ne wanda yake fitar da duburar mutum waje sannan idan aka yi rashin sa’a zai iya zama tamkar kari wanda zai hana mutum sukuni.

Kamar yadda wani likitan Najeriya, Olufunmilayo ya bayyana a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, ya ce hakan na iya janyo Basir.

Kamar yadda ya shaida:

Zama kan shadda na fiye da minti 10 na iya janyo wa mutum cutar Basir.

“Ba don kuna amfani da lemu mai zaki ko sikari ba, Basir yana kama ku ne saboda yadda ku ka mayar da shaddarku wurin danne-dannen waya.

“Idan kuna dadewa a kan shaddarku, yana janyo jijiyoyin duburarku su saki, daga bisani su fara zafi mutum ya rasa sukuni. Wannan cutar ce Basir.”

A kwanakin baya Darektan wata cibiya da ke birnin Los Angeles a kasar Amurka, Samuel Oschin, ya yi wata wallafa mai kama da wannan.

Bayyanar bidiyon kafin auren Furodusa Mai Shadda da amaryar sa yana rungumar ta ya tayar da kura

Fitaccen furodusan Kannywood, Abubakar Bashir mai shadda yana shirin angwancewa da jaruma Hassana Muhammad kamar yadda shi da ita suka sanar a shafukan su ta hanyar wallafa hotunan katin gayyata.

Baya ga wannan, ya wallafa bidiyo na jerin akwatuna 17 na auren su wanda yayi mata a matsayin lefe, hakan ya sa mutane suka tabbatar da cewa shirye-shiryen aure ya yi nisa.

Sai dai a ranar Litinin da yamma wani bidiyo ya karade shafukan sada zumunta wanda aka ga yana rungumar ta da alamun hotunan kafin aure zasu yi, wato Pre-wedding pictures.

Hakan ya yi matukar janyo cece-kuce inda mutane suka dinga suka tare da alawadai akan bayyana alfashar da suka yi.

Kasancewar aure bautar Ubangiji ne, wasu suna ganin bai dace a saba masa ba yayin shagulgulan musamman idan aka yi la’akari da cewa su biyun sanannu ne kuma suna ikirarin fadakarwa suke yi a fina-finai.

Shafin Dokin Karfe Na Facebook ya wallafa bidiyon wanda fiye da mutane dubu 31 suka gani. Sannan daruruwan mutane sun dinga tsokaci daban-daban.

LabarunHausa.com ta tattaro wasu daga cikin tsokacin jama’a:

Wani Abdullahi Yakasai yace:

“Ma su koya Tarbiyya a kasar Hausa kenan…”

Wata Maman Nana ta kada baki ta ce:

“Dagani sun Saba yin haka da juna
Tunda Babu alamar kunya atare da suAllah ya shiryemu baki daya.”Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe