24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

 Allah sarki: Bidiyon tsohon da ya bushe tamkar kwarangal, mutuwa ta manta da shi

Labarai Allah sarki: Bidiyon tsohon da ya bushe tamkar kwarangal, mutuwa ta manta da shi

Hankula sun karkata kan wani tsohon mutum a yanar gizo musamman dandalin TikTok. 

Mutumin mai suna, Luang Por Yai, ya sanya mahawara a dandalin, inda wasu sukayi ta kokarin sai sun gano takamaiman shekarun sa. 


Jikar sa wadda take dora bidiyon sa a yanar gizo ta kawo karshen mahawarar da mafi yawan ma’abota yanar gizo suka kasa amsawa. 


Matasa da yawa suna burin ace sun yi nisan kwana, amma bidiyon tsohon mutumin ya sanya wasu da yawa sake canja ra’ayin son dadewa a raye. 


Tsohon mutumin mai suna Luang Por Yai, ya sami matsayi irin na tauraro a dandalin yanar gizo na TikTok, bayan jikarsa ta fara yada biliyoyin sa a wajejen watan Nuwamban shekarar 2021. A rahoton Snopes 

tsoho mai ran kaefe
tsohon da ya bushe tamkar kwarangal, mutuwa ta manta da shi

Saboda yaushin fatar sa, da kuma kamannin kwarangwal da jikin sa ya nuna, ya sa ma’abota yanar gizo nata mahawara akan yawan shekarun sa, inda har wasu suke barkwancin cewa ko yaya kamannin sa suke a lokacin da aka haifi sarauniya ‘yar zabal, da kuma zamanin Annabi Isah. 


Jikar Luang din ta bayyana hakikanin shekarun tsohon

Jikar sa wadda take amfani da suna @Auyary13 ta bayyana cewa, shekarun kakan nata 109 ne. 

Amma batayi karin bayani ko yanayin bushewar jikin nasa yana da nasaba da wata al’ada ta kunshe jiki da Japananawa ke kira (Sokushinbutsu ) wadda ta samo asali daga masu bauta daga shekarar 1081 zuwa 1903. 


Yawan dora bidiyon sa da Jikar tasa keyi a dandalin nata wanda yake samun miliyoyin masu kallo, ya ja mata samun tururuwar miliyoyin mabiya a dandalin nata.

Ku kalli bidiyoyin a kasa :

https://www.tiktok.com/trending?referer_url=https%3A%2F%2Fwww.legit.ng%2F&referer_video_id=7067463555943025946&refer=embed

@auy.saranya

เมื่อเหลนน้อยมาเรียกหา หลวงตาสัมผัสได้ถึงความรักและห่วงใย เรียกมาเคาะหัวให้พรเหลนเลย สาธุๆๆ🙏🙏

♬ บทเพลงสวดบารมี 30 ทัศ – ocean media

Sharhin ma’abota dandalin yanar gizo akan bidiyon tsohon


@Lilcentasuquo1 yace: 

“Hian, wannan yayi yawa, ina nufin yayi kamar abin tsoro”. 

@lovina61144088 yace :

“Ba zai yiwu ba fa, bana son irin wannan tsufan a kan kaina”

@StellaNnanna yace :

“Kawai shekara 109 amma yake da wannan kamannin,? Mai yiwuwa bashi da lafiya, ba wai kawai tsufan bane”

@RichieB78550327 yace :

“Abin tsoro… Bana fata na kai irin wadannan shekarun, wahala take sha kuma tana wahalar da ‘yayan ta”. 


@purechocky yace:

“Na tabbata wannan irin mutan da dinnan ne masu shanya kansu a rana”. 

Bayan shekaru 42 da tafiya neman arziki, tsoho mai shekaru 94 ya dawo gida wayam

Wani tsoho ya dawo hannu Rabbana, bayan kwashe shekaru 42 yana neman arziki inda ya bar gidan sa da iyalan sa, LIB taruwaito.

Wani dan kasar Kenya mai shekaru 94, ya dawo ga iyalin sa da ke kauyen Majengo, a garin Mwatate da ke yankinTaita-Taveta bayan kwashe shekaru 42 yana neman arziki bayan ya bar gida.

Hiltan Kalugho ya bayar da labarin yadda ya tafi ya bar matarsa da yaransa guda bakwai a gida ya garzaya kasar Tanzania, kasar da ke makwabtaka da su a shekarar 1980 don neman arziki.

A cewarsa:

“Na bar gida na don neman kudin da zan rufa wa kai na asiri don in inganta wa yara na rayuwa . Sai dai, na kasa komawa gida saboda ban samu kudin da nake nema ba.”

Kamar yadda dattijon ya bayyana, ya yi rayuwar a iyakar birnin Mororoni, inda da farko ya fara aiki a matsayin mai hakar ma’adanai, bayan yaga babu wani samu sai ya koma kiwon dabbobi.

“Bayan na ga babu wata riba, kullum cikin kashe ‘yan kudaden nake sai na hakura,” a cewar Kalugho.

Kalugho ya ce, bai sake wani auren ba har ya yanke shawarar komawa gida.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe