35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Allahu Akbar: Hotunan budurwa da ta ciyar da mutum 242 shinkafa da nama a Ramadan sun bayyana

LabaraiAllahu Akbar: Hotunan budurwa da ta ciyar da mutum 242 shinkafa da nama a Ramadan sun bayyana

Wata mata yar Nageriyar ta nuna Soyayyar gaskiya ga mutane lokacin azumin Ramadan, inda tayi karo-karo domin ciyarwa lokaci azumin Ramadan. 

A ranar Laraba 6 ga watan Afirilu, hotunan matar da abincin ya bayyana, inda tace ta shirya abincin mutane 252. 

Yan Nageriya da yawa sun yi mata sharhin godiya a fejin ta, saboda abin kirkin da tayi, wasu kuma idonsu yana kan gunduma-gunduman nama yanka biyu da aka sanya a cikin abincin.

Wata mata yar Nageriya da take sarrafa shafin tuwita mai dauke da sunan, @Nere_Noire, taci gaba da tsarin ta na ciyarwa a watan Ramadan a Wannan shekara ta 2022. A shekarar 2021 ta ciyar da daruruwan mutane. 

ramadan
Hotunan budurwa da ta ciyar da mutum 242 shinkafa da nama a Ramadan sun bayyana

A rana ta hudu 4 ga azumi, matar ta yada hotunan ta inda take kukkulla shinkafa dafa-duka, da namanta har na kimanin mutum 252. 

Bazaku taba jin yunwa ba

A wata daukar, an nuno ta tana zuba abincin a cikin dan soson dauki guzurinka, (take away). Tana addu’a ga duk wanda ta baiwa sadaka, tana cewa bazasu taba tafiya da yunwa ba. 

Daidai lokacin da ake hada wannan rahoton, daruruwan ‘yan Nageriya  sun yi sharhi, inda suke yabawa kokarin matar. 

Jaridar shafin Legit.ng sun tattara sharhi kamar haka:

@gbenguzinsu yace:

“Ko a Ramadhan ko ba a Ramadan ba, yana wahala kaga wasu suna ciyarwa, amma ita tana yin hakan a wannan watan, gaskiya ba karamin abu bane. Abinci shine abu mafi mahimmanci a bukatu, Allah ya saka da miliyiyi “

@badejoTM yace:

” An gaisheki, Allah ya saka miki da alkhairi, amma kina da masallacin da kike rabawa”

@Omo_okunola yace :

“Allah ya yi miki albarka, Allah ya amsa duk addu’o’in ki, ko da yaushe kina kokarin sanya murmushi a fuskar jama’a, kema Allah ya sa bazaki taba yin bakin ciki ba”.

@olaideelegbede yace :”

“Godiya gareka akan abin da kike yi, Allah yayi miki albarka.” 

@slyfoxine yace : 

“Abin da yafi bani sha’awa shine a cikin abincin da akwai gunduma-gunduman nama guda biyu”.

Yadda Muneerat Abdulsalam mai kayan mata ta sha zagi bayan ta nemi a hada mata kudi don tallafa wa talakawa da Ramadan

Fitacciyar mai sayar da magungunan mata, Muneerat Abdulsalam ta sha caccaka da zagi a kafar sada zumuntar Facebook bayan ta nemi tallafi daga mutane don ta taimaka wa talakawa.

A wata wallafar da ta yi a ranar Lahadi, ta bayyana cewa ta sanya lambar asusun bankinta tana neman taimako don tallafa wa masu kananun karfi amma bata samu komai ba sai N1,500.

Kamar yadda ta shaida a wallafa tata:

“Dazun na yi post nace a tura kudi domin a agaza wa talaka, mutum dayane kacchal ya tura naira dubu daya.

“Ba zan iya in saka sunanshi anan ba sabida ban nemi izini ba, haka ma wanda ya turo da dari biyar.

“Na gode maku sosai da yarda da kuma tayyani yin aikin lada, Allah ya amshi ibadan ku, ya kaiku gidan aljanna. Da kuma hanyar taimaka min nima in sami rahamar ubangiji.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe