37.1 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Makudan kudaden da Ronaldo ke biyan budurwar sa duk wata sun kai £10k

LabaraiMakudan kudaden da Ronaldo ke biyan budurwar sa duk wata sun kai £10k
16490806709384
Makudan kudaden da Ronaldo ke biyan budurwar sa duk wata sun kai £10k

Cristiano Ronaldo da Georgina Rodriguez suna ɗaya daga cikin sanannun masoya da suka yi kaurin suna a duniya, suna da miliyoyin mabiya a shafukan sada zumunta tare da samun kudade a wurin tallace-tallacen kamfanoni.

Ta kasance shaharariya a idon duniya musamman a kamfanoni

Ta kasance shahararriyar mai yima kamfanoni tallace -tallace inda akowani talla tana samun jimillar Yuro 8,000 a kowane wata, amma wannan ba shine kuɗin shigarta kaɗai ba.
A cewar wani shirin gidan talabiji na kasar Sipanish mai suna ‘Viva La Vida’, Ronaldo yana tura ma masoyiyar sa adadi kudi kimanin Yuro 100,000 a asusun bankin ta.

Yana tura mata makudan kudade domin kula da tilon ‘yar su

Wadannan makudan kudade yana tura mata ne a matsayin kudin ci da sha,da kuma sauran hidima na tilon ‘yar su kwaya daya, saboda ita ce ke kula da ‘yar tasu idan shi Ronaldo  ba ya nan.

Kwannan Masoyiyar Ronaldo ta fitar da wasu bayanai game da rayuwarta ta yau da kullun akan manhajar Netflix, inda take bayyana yadda take kasancewa uwa, ‘yar kasuwa,kuma mai bada shawarwari duk ita daya.

Abin farin cikin da ba zan taba mantawa da shi ba shi ne ranar mutuwar mahaifiyata, Jaruma Momi Gombe

Jarumar Kannywood, Maimuna Abubakar wacce aka fi sani da Momi Gombe ta ce ranar da ta fi ko wacce rana farinciki a rayuwarta da kuma bakinciki ita ce ranar da mahaifiyarta ta kwanta dama.

Ta bayyana hakan ne a shirin BBC Hausa mai suna Daga Bakin Mai Ita. A ranar 31 ga watan Maris din 2022 ne BBC Hausa ta wallafa bidiyon tattaunar da ta yi da jarumar
Da farko ta fara da gabatar da kanta inda ta ce ta yi firamare da sakandare a garin Gombe. Sannan duk rayuwarta a cikin garin ta yi, sai yanzu kuma sana’a ta mayar da ita garin Kano.

Ta bayyana yadda ta fara fim

Ta shaida yadda ta shiga fim ta hannun wani mai gidanta Usman Mu’azu, kuma dan garinsu ne sannan ya saba da ‘yan uwanta.

Ta ce idan ‘yan fim suna aiki yana burgeta hakan yasa idan aka aiketa kai musu abinci take tsayawa ta dinga kallonsu. Daga nan ya sanyata a shirin.
Ta ce ya tuntubi mahaifiyarta daga nan ta amince inda aka sanyata ta fara shirin fim. Ta ce tana matukar farinciki da alfahari da wakar Jarumar mata wacce suka yi bidiyon da Hamisu Breaker.

Ta ce babu wata soyayya da ke tsakaninta da Mawaki Breaker, kawai mutane ne suka fadin hakan.

Sunusi Oscar 442 ne mai gidanta nan a Kannywood kuma babanta, sannan shi ne darektan da ta fi so.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe