24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Ki yi amfani da kudin da kike sawa a waya kina gulma wurin siya wa kanki turare saboda wari kike yi, Jarumin Kudu ga abokiyar sana’arsa

LabaraiKi yi amfani da kudin da kike sawa a waya kina gulma wurin siya wa kanki turare saboda wari kike yi, Jarumin Kudu ga abokiyar sana’arsa

Fine Boy, jarumin Nollywood Frederick Leonard ya kira wata abokiyar sana’arsa da mai warin jiki, shafin KemiFilani.ng ya ruwaito.

Tauraron fina-finan, wanda a zahiri ya kasa jure irin warin da jarumar (wacce bai ambaci sunanta ba)yayin gudanar da shirin ya sanar da ita a kafar sada zumunta.

frederick
Ki yi amfani da kudin da kike sawa a waya kina gulma wurin siya wa kanki turare saboda wari kike yi, Jarumin Kudu ga abokiyar sana’arsa

A saboda haka ne, Frederick Leonard ya yi amfani da shafinsa na Instagram wajen yi ma ta terere, inda ya ce da ita tayi amfani da kudin da take kashewa wajen gulma yadda ya dace.

“Ya kamata doka ta fara hukunta marasa amfani da turaren kamsasa jiki!

“Musamman idan aikin ka na cudanya da jama’a ne, kuma yana bukatar motsa jiki. Kana iya yin gumi ko idan kayi gumi, kana wari. Ba laifi bane.

“Komin kankantar kudin da kake samu, kana iya jure siya. Yi amfani da kudin da kike kashewa wajen kiraye-kiraye da siyan data don ziyartar shafukan tsegumi a kafafan sada zumunci ki gyara kanki ko kyayi kanshi. Don kada ki halaka abokan aikin ki. Nagode.”

Bayan wallafar, wasu daga cikin abokan aikinsa sun gasgata abunda ya fada, yayin da wasu suka dinga dariya.

‘Yan kudu sun hau fargaba akan ko dai Genevieve ta musulunta bayan ta yi wallafa da ayar Qur’ani, dadduma da kabari

Jarumar masana’antar fina-finan kudu, Genevieve Nnaji ta saki wani gajeren bidiyo a shafin ta na Instagram ya tayar da kura inda aka dinga musayar ra’ayi dangane da bidiyon, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Gajeren bidiyon ya nuna tunatarwa ne akan cewa duniyar nan ba komai bace ba a harshen turanci.

A bidiyon an nuna cewa lahira ce tabbatacciya kuma komai na duniyar nan mafalki ne ba gaskiya ba.

Bidiyon ya nusar da mutane akan su farka, kuma an sanya ayar Al’Qur’ani mai girma da kuma dadduma.

Kamar yadda ake fadi a cikin bidiyon:

“Don Allah! Don Allah! Ku farka! Ku farka! Ku farka! Ko wanne mai rai mamaci ne.”

Bayan ta wallafa bidiyon nan, ya zama abin surutu da kuma fargaba, inda masoyanta musamman ‘yan kudu suka hau cece-kuce.

Sun yi fargaba akan kada fa ace jarumar nan ta musulunta ko kuma shirin musulunta take yi, idan ba haka ba, tana kirista, mai zai hada ta da wallafa ayar Qur’ani, dadduma ko kuma makabarta?

Duk da dai a bangaren story ta wallafa bidiyon kuma bayan awa daya story ke bata a Instagram. Amma sai wata ma’abociya instagram mai suna poshjournal ta kwafo kuma ta wallafa.

Kamar yadda ta wallafa:

“Mafarki ne kawai, Jaruma Genevieve Nnaji ta wallafa bidiyo da Qur’ani, dadduma da makabarta. Allah dai yasa jarumar kalau take.”

Nan da nan mabiyanta suka dinga cece-kuce, wasu suna fargabar kada fa ace musulunta ta yi, wasu kuma suna cewa ai a Najeriya kowa yana da damar yin addinin da ya ga dama. Akwai wadanda suke ganin wallafa ce ta tunatarwa ba wata manufa ba ta daban.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe