27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Ana ta zungurar Sheikh El-Zakzaky bayan ya ce da kan shi ya mayar da idonsa bayan sojoji sun cire masa da bindiga

LabaraiAna ta zungurar Sheikh El-Zakzaky bayan ya ce da kan shi ya mayar da idonsa bayan sojoji sun cire masa da bindiga

Fitaccen malamin addini na garin Zaria, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya bayyana irin badakalar da suka yi da sojoji yayin rikicin da suka sha da sojoji.

Idan ba a manta ba, a shekarun baya rikici ya barke tsakanin El-Zakzaky da sojoji wanda lamarin ya kazanta kwarai.

elzakzakkkty
Ana ta zungurar Sheikh El-Zakzaky bayan ya ce da kan shi ya mayar da idonsa bayan sojoji sun cire masa da bindiga

Sakamakon fadan, yaransa da almajiransa da dama sun halaka sannan gwamnati tadauke shi ta sakaya.

Bayan kwashe shekaru ana shari’a tsakaninshi da gwamnatin Jihar Kaduna, an sako shi wanda alamu sun nuna yadda shi da matarsa suka raunana.

Bayan fitowarsa daga hannun hukuma ne ya samu damar tattaunawa da manema labarai wanda ya bayyana yadda ya sha wahala da harbe-harbe a wurin sojoji.

A cewarsa kamar yadda wani guntun bidiyo wanda ya dinga yawo a kafafen sada zumunta:

“Amma ban san yadda aka yi bullet ya yi kwana ya harbi idona ta gefe daga idon dama ya koma fincike idon hagu na dauki idon na mayar na matse na kwaso jinin da ke hannu na na danne.”

Mutane da dama sun dinga karyata wannan labarin na shi karkashin wallafar da wani ma’aboci amfani da kafar Facebook, Sada Suleiman Usman.

LabarunHausa.com ta tsinto wasu tsokacin jama’a:

Wani Shu’aibu Alkali ya ce:

“Ayi ma Malam uzuri fa.

Ga shekaru ga kuma kashe yaransa.Dole mutum ya rude gaskiya.”

Hassan Ba Wasa Gama ya ce:

“Mutumin nan fa ya haukace da alama.”

Bulama Adamu ya ce:

“Mutimin da yake yiwa Sahabbai kazafi dan ya shararo wannan ai ba abin mamaki ba ne.”

Mansur Abubakar Kwargaba ya ce:

“Naga anata yada labarin ban yarda ba
Wlh duk dauka ta fake news ne
Subhanallah ashe da gaske ne ya fadi hakan
Sannu fah malam.”

El-Zakzaky: Za mu maka gwamnatin Kaduna gaban kotu – Lauya

A jiya ne dai wata babbar kotu a jihar Kaduna ta wanke ta kuma sallami shugaban kungiyar ‘yan uwa Musulmai, wato Shi’a na Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zeenat.

Bayan zaman awa takwas da aka shafe a kotun, Alkalin Kotun Gideon Kurada, ya sallami sauraron karar, inda yace masu gabatar da karar sun kasa gabatar da kwararan shaidu akan wanda suke karar.

Sama da shekara hudu, El-Zakzaky da matarsa Zeenat na hannun jami’an tsaro inda ake zargin su akan laifuka guda takwas, da suka hada da kisan kai, tada zaune tsaye, da dai sauran su duka wadanda gwamnatin jihar Kaduna ke zargin su da shi.

Lauyan wanda ake kara, Marshal Abubakar wanda ya wakilci shugaban lauyoyin wanda ake karar a kotun Femi Falana, SAN, ya bayyanawa manema labarai cewa:

Shari’ar Sheikh EL-Zakzaky da matarsa Zeenat ta zo karshe bayan kotu ta wanke su daga laifukan da gwamnatin jihar Kaduna ke tuhumar su da shi.

Kotun ta gano cewa laifin da ake zargin shi da aikatawa a shekarar 2015, ana neman ayi amfani da dokar da aka sanya a shekarar 2017 a yi masa hukunci da ita. Alkalin kotun Gideon Kurada, ya bayyana cewa tun farko ma bai kamata a shigar da wannan kara ba, saboda gwamnati bata da hurumin kama wani akan abinda ba lalifi bane a lokacin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe