24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Harin jirgin ƙasa: Ba zamu huta ba har sai mun dawo da fasinjojin da aka ɗauke, Gwamnatin tarayya

LabaraiHarin jirgin ƙasa: Ba zamu huta ba har sai mun dawo da fasinjojin da aka ɗauke, Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta tabbatar wa iyalan fasinjojin jirgin ƙasan da yan ta’adda su ka ɗauke satin da ya wuce, cewa zata yi iyakar bakin ƙoƙarin ta wajen ceto mutanen cikin ƙoshin lafiya. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Gwamnatin tarayya ta bayar da tabbacin ceto fasinjojin

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, shi ya bayar da wannan tabbacin ga iyalan waɗanda lamarin ya ritsa da su a wurin taron manema labarai na ministoci da aka saba shiryawa a babban birnin tarayya Abuja ranar Alhamis.

A makon da ya gabata ne, wasu ‘yan ta’adda suka farmaki Jirgin ƙasan zirga-zirgar sa a tsakanin Abuja-Kaduna, inda suka kashe mutum 8,  sannan su ka yi garkuwa da mutane da yawa daga cikin fasinjojin.

Amaechi, wanda ƙaramar ministan Sufuri, Gbemisola Saraki ta wakilta, ya bayyana cewa ma’aikatarsa na cigaba da tuntubar hukumomin tsaro akai-akai domin ganin an ceto mutanen da harin ya ritsa da su.

Fasinjoji
Ministan sufuri, Mr Rotimi Amaechi.

Sai dai, ministan kuma yayi nuni da cewa ba zai yuwu ya ba da cikakken bayani kan shirin da su ke yi da hukumomin tsaro domin kaucewa dawo wa da hannun agogo baya.

Iyalan fasinjojin sun nuna ɓacin ran su

Wasu iyalan fasinjojin waɗanda lamarin ritsa da su sun je har wurin taron ministocin domin nuna fushin su kan gazawar gwamnati na ceto mutanen kwanaki 12 bayan aukuwar lamarin, inda su ka ƙalubalanci gwamnati kan cewa lallai ta ƙara zage ɗamtse.

Yadda na sha da ƙyar a harin jirgin ƙasan Kaduna-Abuja, Rahama Sadau

Shahararriyar jarumar fina-finan Najeriya, Rahama Sadau tare da iyalan ta sun godewa Allah bayan da jarumar ta wallafa yadda ta samu ta tsira daga harin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja. Jaridar Daily Trust ta rahoto

An kai ma jirgin ƙasan hari

A daren ranar Litinin, ‘yan ta’adda sun kai hari ga jirgin ƙasan kan hanyar sa ta zuwa Kaduna. Sun saka bam a hanyar jirgin wanda hakan ya sanya dole jirgin ya tsaya.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan daga baya sun zagaye kusan ilahirin jirgin sannan su ka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, wanda hakan ya janyo mutane da dama su ka rasa ran su.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe