27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Nasrun minAllah: Sojoji sun sheƙe ‘yan ta’adda 80 a yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiya

LabaraiNasrun minAllah: Sojoji sun sheƙe 'yan ta'adda 80 a yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiya

Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa dakarun soji sun halaka ‘yan ta’adda sama da 80 a cikin sati biyu a yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiya. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Darektan watsa labarai na hukumar, Maj. Gen. Bernard Onyeuko, ya bayyana hakan lokacin da ya ke wa manenma labarai ƙarin haske akan ayyukan soji daga 25 ga watan Maris zuwa 7 ga watan Afrilun 2022, ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja.

An halaka ‘yan ta’adda da dama

A jihohin Kaduna da Neja, Onyeuko ya bayyana cewa sojojin da ke atisayen “Operation Thunder Strike” sun halaka ‘yam ta’adda 34 sannan sun ƙwace bindigu ƙirar gida guda 17 da kuma mashina 17 a lokacin.

Ya bayyana cewa sojojin sun samu nasara ne lokacin da jiragen yaƙi su ka jefa bama-bamai a ranar 30 ga watan Maris, ga ‘yan ta’addan da su ke tafiya zuwa hanyar Akilibu-Sarkin Pawa a ƙauyen Mangoro, a tsakanin jihar Kaduna da Neja.

Jiragen yaƙi sun yi ɓarin wuta

Ya bayyana cewa jiragen yaƙi sun halaka ‘yan ta’adda da dama bayan sun tare su.

Ya ƙara da cewa an hango ‘yan ta’adda da dama a kusa da Kusasu, bayan wani sintirin jiragen su ka gudanar inda aka buɗe musu wuta a ranar 31 ga watan Maris, sannan su ka halaka sama da ‘yan ta’adda 33.

A ƙarƙashin atisayen “Safe Haven”, jami’in ya bayyana cewa sojoji suna cigaba da samun nasarori masu ɗumbin yawa.

Sojoji sun kashe ‘yan bindiga da yawan gaske yayin da suke tsaka da shagalin bikin shugabansu a Katsina

Yan bindiga da dama sun rasa rayukan su yayin da sojojin sama, NAF suka dinga ragargazar su yayin da suke bikin daya daga cikin shugabannin su a Jihar Katsina, Jaridar Leadership ta ruwaito.

Cikin wadanda aka halaka har da Sule, wani shu’umin dan bindiga, wanda dan uwan Lalbi Ginsha ne, shi ma gagarumin dan ta’adda ne.

Kamar yadda PRNigeria ta ruwaito, lamarin ya auku ne a kauyen Unguwar Adam da ke karamar hukumar Dan Musa a Jihar Katsina.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe