35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Najeriya ce kasa ta 3 a duniya da ke kan gaba wajen cin naman kare

LabaraiNajeriya ce kasa ta 3 a duniya da ke kan gaba wajen cin naman kare
Dog meat
Najeriya ce kasa ta uku a duniya da ke kan gaba wajen cin naman kare

Shin kun san cewa Koriya ta Kudu, Kasar Vietnam da Najeriya sune manyan ƙasashe uku da suke kan gaba wajen sarafa naman kare? Waɗannan su ne binciken wani rahoto da ya bayyana kwanan nan na Matthew Nash, wani jagoran bincike mai zurfi akan kasashen da suka fi ta’ammali da Kare, yana nuna mafi kyawun ƙasa kuma mafi muni kasar da take harka da naman kare a shekarar 2022.

kasar Najeriya tana cikin kasashen da cin naman kare yazamo kamar wani nau’i abincin al’ada

Kasashe da dama, ciki har da Najeriya, sun kasance kasashe da suka dade suna ta’ammali da naman kare, wanda hakan sun dauke shi kamar wani bangare na al’adarsu ta bangaren abinci.

A kasar Chana, bukukuwa da dama suna more cin naman karen su.
Bugu da kari kuma,Mista Nash ya shaida wa jaridar PREMIUM TIMES cewa, akwai wasu muhimman abubuwa guda bakwai da yayi amfani dasu wajen zakulo kasashe 51 da ke da bayanan da akayi amfani da su wajen zakulo kasahsen da sufa ta’ammali da karen .”

Wadannan kasashe suna kokarin kare hakkin dabbobi irin karnuka

Waɗannan abubuwan sun haɗa da haƙƙin dabba, otal ɗin dabbobi, wadatar likitocin dabbobi, kariyar dabbobi, haɗarin kamuwa da cuta, sanin jin daɗin dabba da abokantakar dabbobi.

Ƙasashen da aka fitar da sunayen su a cikin rahoto mai taken ’51 Mafi Yawan Ƙasashe Masu masu ta’ammali da naman kare a cikin shekarar 2022,’wanda aka fitar a ranar 25 ga watan Maris, 2022, an zaɓi su ne bisa la’akari da bayanan da ake da su.
Saboda kasashe da yawa ba su da cikakkun bayanai game da kula da dabbobi, musamman karnuka, masu binciken sun yi amfani da hanyoyin mabanbanta.

Abin mamaki, Najeriya ta kasance ta 45 a cikin kasashe 51 da ke cikin jerin sunayen, inda ta samu maki 44.41.
A gefe guda kuma, ƙasashe kamar Italiya, New Zealand, Faransa, UK, da Jamus sun kasance a matsayin ƙasashe biyar wanda suke kan gaba wajen ta’ammali da karnuka,inda kowannensu yana da maki sama da ɗari uku.

Kowace daga cikin wadannan ƙasashe suna da dokar kare dabbobi da abubuwa daban-daban waɗanda za su iya hana haɗarin cutarwa ga wadannan abin amfanin yau da kullum.
Bugu da kari Waɗannan ƙasashe sun sami sakamako mai kyau wajen yakar cutar haukar kare, da kuma ingantattun asibitin dabbobi, da wuraren kwana na dabbbobin.

Bugu da ƙari, ba su da yawan yawan cin naman kare.

Ubangiji ke tsiro da ganyen wiwi, ban ga laifi ba don an yi amfani da shi, Jarumin fim kuma Fasto Majid Michel

Fitaccen jarumin Nollywood kuma fasto, Majid Michel ya ce Ubangiji ne ya ke tsiro da ganyen wiwi daga kasa don haka bai ga laifi ba don an yi amfani da shi ba, LIB ta ruwaito.

Yayin da yake bayani da Kent Mensah a gidan rediyo Asaase, Majid ya yi kira ga gwamnatin kasar Ghana da ta amince da saye gami da siyarwa tare da amfani da wiwi a kasar.
Kamar yadda yace:

“Na yi shaye-shaye a baya. Ba wai ina nufin wiwi ba. Amma ban ga laifin amfani da wiwi ba, Ubangiji ne ya ke tsiro da ita, kuma ya ke halittarta.”

Ya bayyana yadda ya yi shaye-shaye a shekarun baya, inda ya ce bai taba ganin wanda ya sha wiwi ya yi mankas ba.
A cewarsa:

“Ban taba jin wanda wiwi ya yi wa yawa ba. Na sha wasu kayan shaye-shayen kamar hodar iblis da sauransu.

“Na sha abubuwan da idan yanzu na fada muku sai kun yi mamaki. Tsawon shekaru inata kokarin ganin na daina shaye-shaye.”

Majid ya ba matasa masu kasa da shekaru 25 da su kiyaye amfani da ganye. Ya shawarce su da su dinga yin shayi da ganyen maimakon amfani da hayakin shi.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe