Abubuwan da ke ciki
Wata yarinya ƴar shekara 12 a duniya wacce wani malamin makaranta yayi wa fyaɗe a unguwan Fantaro cikin ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna, a wajajen watan Yunin 2021, ta haifi ɗa namiji. Jaridar Daily Trust ta rahoto.
Malamin ya yaudare ta sannan yayi mata fyaɗe
Halima (ba sunanta na gaskiya ba) tana sayar da chin-chin, a ƙauyen su, lokacin da malamin mai suna Salihu ya yaudare ta cewa zai sayi chin-chin na N200.
Salihu ya rufe mata baki sannan yayi mata fyaɗe a cikin ɗakin.
Daily Trust ta samo cewa yarinyar ta ɗauki juna biyu watanni uku bayan aukuwar fyaɗen, inda aka miƙa ta a hannun ministirin jinƙai da walwala ta hannun gidauniyar Ummulkhairi Foundation.
An tabbatar da haihuwar yarinyar
Sai dai, yayin da ta ke tabbatar da haihuwar yarinyar, kwamishiniyar jinƙai da walwala ta jihar, Hajiya Hafsat Baba, ta bayyana cewa yarinyar ta haifi ɗa namiji cikin nasara.
Hajiya Hafsat Baba ta ce:
Ƙaramar yarinyar ta haifi ɗa namiji sati uku da su ka wuce, sannan ina farin ciki cewa likitoci a asibitin Barau Dikko sun bata kulawa ta haihu da kanta ba tare da an yi mata aiki ba.
Duk da dai jaririn yana hannun mu, mun miƙa ta zuwa wajen mahaifiyar ta ranar Laraba. Sai dai ba za mu yi ƙasa a guiwa ba wajen ganin mun ƙwato mata haƙƙin ta a wurin wannan mutumin da ya jefa ta cikin wannan halin.
Ta yi nuni da cewa malamin yana garƙame a wurin hukuma tun lokacin da lamarin ya auku.
Borno: ‘Yan sanda sun cafke saurayin da ya yiwa tsohuwa mai shekaru 92 fyade
Hukumar ‘yan sandan jihar Borno, ta cafke wani Zakariya Ya’u, bisa laifin yin fyaɗe ga wata mata mai shekaru 92 a duniya.
An bayyana yadda yayi mata fyaɗe
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mr Abdu Umar, ya bayyana a wata sanarwa ranar Alhamis 31 ga watan Maris cewa Ya’u ya aikata laifin ne a yankin Mufa “A” na ƙaramar hukumar Askira Uba a jihar. Shafin LIB ya rahoto
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]