29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

Duk da wasan kwaikwayo nake yi, ba na fim din da zai zubar da mutunci na, Jarumin Kannywood, Isa Bello Ja

LabaraiKannywoodDuk da wasan kwaikwayo nake yi, ba na fim din da zai zubar da mutunci na, Jarumin Kannywood, Isa Bello Ja

Fitaccen jarumin Kannywood Isa Bello Ja wanda aka fi sani da Dattijon arziki ya ce duk da ya san shirin fim yake yi amma ba ya yin role din da ya san zai zubar masa da mutunci.

Ya bayyana hakan ne a wata zantawa da BBC Hausa ta yi da shi a wani shirinta na Daga Bakin Mai Ita wanda ta ke tattaunawa da manyan jarumai da sanannun mutane.

dattijo

Kamar yadda ya fara da gabatar da kansa, inda ya ce:

“Sunana Isa Bello Ja wanda aka fi sani da Dattijon Arziki. A Kano na tashi, a Kano na girma, na yi aure, karatu kuma a Kano na yi duk rayuwata.”

Ya ce ya yi karatun addini da na boko kadan amma mu’amula da mutane ta sa ya goge sosai da rayuwa. Ya ce a Sokoto aka haife shi amma sai daga baya suka dawo Kano.

Ya ce shekarunsa 70 yanzu haka don an haife shi a 1952. Kuma matarsa daya. Yaransa 10 kuma yana da jikoki.

Yayin da aka tambaye shi dalilin da ya sa ake ce masa dattijon arziki, ya bada amsa da:

“Dattijon arziki shi kuma akan wannan dramar ce na samu Dattijon arziki. Na yarda ni mai wasan kwaikwayo ne amma ban dauki wasan kwaikwayo a matsayin wasa ba.

“Saboda haka na rike wani bangare na ce duk wani role wanda za a bayar wanda bai dace da mutunci na ba da al’adata ba, ba zan yi ba.

“Na yarda ba zan yi barawo ba, ba zan yi dan daudu ba, ba zan yi kawali ba, ba zan yi dan giya ba, ba zan yi mai neman mata ba, ba zan yi dan caca ba, ba zan yi mai kunna sigari ba, wanda za aga yana shanawa ko yana wani abu.

“Abunda na yarda duk role din da zan yi ya dace da kamanni na da al’ada ta. Don babu abunda nake so a rayuwata fiye da mutunci na.”

Ya ci gaba da cewa kullum addu’arsa guda 3 ce, yana fatan Ubangiji ya inganta imaninsa, da lafiyarsa da kuma mutuncinsa.

Ya ce hakan ya sa ba ya wasa da mutuncinsa, saboda bai dace a amshi kudi kadan ko mai yawa ba don ka zubar da mutuncinsa.

Ya ce ya fara fim tun 1976. Lokacin yana shirin fim din talabijin. Daga bisani ya yi aiki a wasu gidajen talabijin kafin ya dawo su fara Kannywood.

Na wanke wa jarumai mata bireziyya da dan pant, inji Jarumi Mustapha Naburaska

Fitaccen jarumin barkwanci, Mustapha Naburaska ya bayyana a irin wahalhalun da ya sha a masana’antar Kannywood kafin ya kai wannan matakin da yake a yanzu a wata hira da Arewa 24 ta yi da shi a cikin shirin Gari ya waye inda ya amsa tambayoyi da dama.

A cikin hirar, Naburaska ya bayyana cewa a baya ba ya da wata daraja a masana’antar Kannywood sai dai a aike shi siyo sigari, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Ya ci gaba da bayyana cewa har wankin bireziyya da dan pant ya yi wa manyan jarumai mata. Ya ce har rikon jaka ya yi musu a lokacin ba ya da wata daukaka.

A cikin bayanin da jarumin ya yi, ya bayyana yadda ake je da shi don sanya shi cikin waka, inda mashiryin shiri Rabi’u Ibrahim ya wulakanta shi.

A cewarsa, ya ce shi bai ga jarumin da za a sanya a wakar ba. Dama manyan jarumai suna bayar da labarin yadda masu shirya shiri suke raina musu wayau tare da wulakanta su.

Yanzu haka da yawan su sun zama manyan jarumai, shi kuma furodusan yana nan babu wanda ya san da shi a yanzu kuma ya ma bar harkar fim din.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe